| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Wata ƙungiyar Faransa da ke goyon bayan Falasɗinawa ta yi kira a ƙaurace wa dabinon Isra’ila
Shugabar Ƙungiyar EuroPalestine da ke Faransa ta ce ƙaurace wa waɗannan kayayyakin zai yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin Isra'ila.
Wata ƙungiyar Faransa da ke goyon bayan Falasɗinawa ta yi kira a ƙaurace wa dabinon Isra’ila
Ƙungiyar ta ƙara kaimi a kiraye-kirayenta na ƙauracewa kayayyakin Isra'ila a lokacin watan Ramadan / AP
6 awanni baya

Ƙungiyar EuroPalestine da ke Faransa ta yi kira a ƙaurace wa dabino da ake samarwa daga matsugunan da Isra'ila ta mamaye ba bisa ƙa'ida ba a Yammacin Kogin Jordan kuma ake sayarwa a ƙasar.

Ƙungiyar, wacce ke fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawa, ta ƙara ƙaimi a kiraye-kirayenta na neman a ƙaurace wa kayayyakin Isra'ila a lokacin watan Ramadan, lokacin da amfani da dabino yake ƙaruwa sosai.

A ranar Laraba ne shugabar ƙungiyar, Olivia Zemor, ta bayyana cewa ana sayar da wani nau’in dabino mai yawa daga kamfanin Medjool a Faransa "kuma ya fito ne daga yankin matsugunan da Isra'ila ta mamaye ba bisa ƙa'ida ba ko kuma daga kamfanoni da ke da hannu a mamayar."

A cewar Zemor, wasu daga cikin akwatuna da aka adana dabinon suna nuna Jordan ko Maroko a matsayin ƙasar da aka samo su na asali, amma ainihin kayayyakin daga Isra'ila suka fito.

Wayar da kan jama'a a manyan kantuna

Ta bayyana cewa, a wani ɓangare na gangamin ƙaurace wa kayayyakin Isra’ila, wasu masu sa-kai suna gudanar da ayyukan wayar da kan jama'a a manyan kantuna don sanar da su, tana mai cewa manufar ita ce ƙarfafa wa mutane gwiwa don su daina sayen kayan da Isra’ila ta samar.

Ta kuma bayyana cewa, ƙarƙashin ƙa’idojin Faransa ‘yan kasuwa ko masu sayar da kayayyaki sukan nuna ainihin ƙasar da ko wanne irin kaya ya fito, musamman na busassun ‘ya’yan itatuwa.

Zemor ta kuma jaddada cewa ba za su iya sanya kayayyakin da suka fito daga yankunan Falasɗinu da aka mamaye a matsayin "Isra'ila" ba.

Ta ce ƙaurace wa waɗannnan kayayyakin zai yi matukar tasiri ga tattalin arzikin Isra’ila, ta na mai ƙari da cewa wasu kamfanonin abinci na ƙasashen duniya su ma sun bi ‘‘tsarin ƙauracewar.’’

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza ya kashe mutane fiye da 72,000, galibi mata da yara, tare da jikkata fiye da 171,000 tun daga watan Oktoban 2023.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a watan Oktoban bara, sojojin Isra'ila sun keta ɗaruruwan doka ta hanyar hare-hare da harbe-harbe, inda suka kashe Falasɗinawa aƙalla 603 tare da jikkata 1,618 tun daga lokacin, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinawa a Gaza.