| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Samamen ya kuma kai ga ƙwace na’urori 303 tare da gano wasu mutane 117 da ake zargin an yi safarar su daga Nijeriya zuwa Ghana, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Ghana ya ruwaito.
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Ghana

Hukumomin Ghana sun kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifukan intanet a Sasaabi, wani yanki na birnin Accra, bayan wani bincike ya gano cewa mutane 89 sun yi asarar kusan dala miliyan 8.3 sakamakon damfarar intanet.

Samamen ya kuma kai ga ƙwace na’urori 303 tare da gano wasu mutane 117 da ake zargin an yi safarar su daga Nijeriya zuwa Ghana, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Ghana ya ruwaito.

Kamen na cikin wani shirin haɗin gwiwa na ƙasashe daban-daban mai suna Joint Disruption Week, wanda hukumomin tsaro da kamfanonin fasaha suka gudanar domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifukan intanet a ƙasashen Yammacin Afirka.

A cewar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, aikin haɗin gwiwar ya kai ga kama mutane 28 a Ghana da Nijeriya, tare da cire asusu, shafuka da ƙungiyoyi na bogi miliyan 3.7 daga intanet. Haka kuma, an gano kuɗaɗen da suka haura dala miliyan 11 waɗanda ake shirin daskararwa.

A Nijeriya, hukumomi sun kama mutane tara tare da ƙwace na’urori 53 yayin samamen.

Hukumar Yaƙi da Laifukan Intanet ta Birtaniya ce ta jagoranci aikin daga Landan, tare da haɗin gwiwar hukumomin Amurka, Birtaniya, Ghana da Nijeriya, da kuma ƙungiyar ’yan sandan ƙasa da ƙasa ta INTERPOL da kamfanonin fasaha.

Binciken ya mayar da hankali kan cibiyoyin damfara da ake zargi da hannu a laifuka da suka haɗa da damfarar jarin kuɗaɗen intanet, da kuma kwaikwayon jami’an tsaro domin yaudarar mutane ko yi musu barazanar kama su.

Wata dabarar damfara da aka fi sani da Pig Butchering ma na daga cikin hanyoyin da ake bincika. A irin wannan damfara, masu laifi kan gina dangantaka da waɗanda suke son damfara kafin su shawo kansu su zuba kuɗi a shafukan saka jari na bogi, musamman waɗanda ke da alaƙa da kuɗaɗen kirifto.

Hukumomin Amurka sun ce samamen ya nuna muhimmancin haɗin gwiwar ƙasashe wajen yaƙi da damfarar intanet, wadda masu aikata ta kan kasance a wata ƙasa yayin da suke damfarar mutane a wasu ƙasashe.

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta ce cibiyarta da ke karɓar rahotannin laifukan intanet ta samu rahotanni 72,984 na damfara a shekarar 2025. A cewar hukumar, damfarar jarin kuɗaɗen kirifto ta kai kashi 72 cikin 100 na irin waɗannan rahotanni.

Hukumomin sun ce za su ci gaba da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya da kamfanonin fasaha domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka, gano kuɗaɗen da aka sace da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.