Aƙalla mutane 17, ciki har da yara da tsofaffi, aka kashe yayin wani hari da 'yanbindiga suka kai ranar Laraba da daddare a wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato a tsakiyar Nijeriya, a cewar rundunar ‘yansandan ƙasar.
Harin, wanda rahotanni suka ce an kai shi a yankin Tafi Gana, wani ƙauye da ke Kyie Ihwien, kusa da Jebbu Miango, ya kuma jikkata mutane huɗu, waɗanda ke karɓar magani a wasu asibitoci a halin yanzu.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yansandan Jihar Filato, SP Alfred Alabo ya fitar ranar Alhamis, ta ce bayan samun rahoton harin, rundunar ta gaggauta tura jami'anta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Sai dai ya ce da maharan sun tsere cikin dazukan da ke yankin bayan sun hango jami'an 'yansanda.
“Binciken farko da jami'anmu suka gudanar ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:55 na daren ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, lokacin da wasu mutane ɗauke da makamai suka kutsa cikin al'ummar tare da buɗe wuta kan mazauna yankin.
Sakamakon haka ne mutane 17 suka rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka samu munanan raunuka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa ta musamman, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a mutuware domin ci gaba da bincike.”
Rundunar 'yan sandan ta kuma ce kwamishinan 'yansandan Jihar, CP Sunday Okoebor, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ta himmatu wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan hari.
Kazalika wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ƙungiyar Ci-gaban Al'ummar Irigwe (IDA), Sam Jugo ya fitar, ta bayyana cewa maharan na ɗauke da manyan bindigogi da wasu makamai masu haɗari.
A cewar ƙungiyar, lamarin ya jefa mazauna yankin cikin firgici, inda aka gano gawarwakin mutane kusan 16 a wayewar safiyar ranar Alhamis.
Basaraken yankin, Nggwe Gado Dama, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai rahoton harin ga ofishin 'yansanda na Ƙaramar Hukumar Bassa da na kwamandan rundunar Operation Enduring Peace ta sashe na uku.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin da harin ya auku a lokacin da aka fitar da wannan sanarwar.
Ƙungiyar Ci-gaban Al'ummar Irigwe ta yi Allah wadai da kisan, tare da kira ga mazauna yankin da kada su yi gaban kansu wajen ɗaukar fansa, inda ta buƙace su da su bai wa jami'an tsaro damar gudanar da bincike da hukunta waɗanda ke da hannu a harin.
Haka kuma, ƙungiyar ta miƙa ta’azziyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Rigwe baki ɗaya bisa wannan babban rashi.















