| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC)
An naɗa Farfesa Mustapha Aliu domin wakiltar yankin Arewa maso Yamma, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru, yayin da Bashir Muhammed Umar zai wakilci yankin Arewa ta Tsakiya, don maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu.
Shugaba Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe a Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC)
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance waɗanda aka zaɓa kafin yanke hukuncin amincewa ko ƙin amincewa da naɗe-naɗensu.

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya zaɓi mutum huɗu a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da wasu mutum biyu a matsayin Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs), domin cike guraben da ake da su sakamakon ƙarewar wa’adin wasu jami’an hukumar.

Waɗannan naɗe-naɗe, waɗanda ke buƙatar tantancewa da amincewar Majalisar Dattawa, sun haɗa da sake naɗa Dr. Bala Bila a matsayin Kwamishinan Ƙasa mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas.

An naɗa Farfesa Mustapha Aliu domin wakiltar yankin Arewa maso Yamma, inda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru, yayin da Bashir Muhammed Umar zai wakilci yankin Arewa ta Tsakiya, inda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu.

Tinubu ya kuma zaɓi Oluwatoyin Babalola, wadda a halin yanzu ita ce Kwamishiniyar Zaɓe ta Jihar Osun, a matsayin kwamishiniyar ƙasa mai wakiltar yankin Kudu maso Yamma. Ana sa ran za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba.

Mutum biyun da aka zaɓa domin mukaman Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs) su ne Dr. Samuel Akinjide Akinleye, tsohon babban sakatare mai ritaya, wanda aka zaɓa domin wakiltar Jihar Ekiti, da kuma Zahradden Basiru Sanusi daga Jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.

Shugaban ƙasar ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta gaggauta kammala aikin tantancewa da tabbatar da naɗe-naɗen, gabanin babban zaɓen da ake shirin gudanarwa a watan Janairu.

Waɗannan naɗe-naɗe sun zo ne a daidai lokacin da INEC ke shirye-shiryen babban zaɓen ƙasar, inda ake sa ran naɗawa da tabbatar da kwamishinonin zai taimaka wajen cike guraben da ke cikin shugabancin hukumar.

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance waɗanda aka zaɓa kafin yanke hukuncin amincewa ko ƙin amincewa da naɗe-naɗensu.

 

 

Rumbun Labarai
’Yanta’addan Boko Haram sun kashe sojoji 10 a harin da suka kai wani sansanin soji a Nijeriya
Zaɓen Nijeriya na 2027: Ba ko ina zan bi tawagar yaƙin neman zaɓen APC ba – Tinubu
IMF ya gargaɗi Nijeriya kan mayar da tallafin man fetur
Cocin Katolika a Nijeriya ta rufe makarantu da asibitinta a jihar Benue saboda matsalar tsaro
NDLEA ta kama mutum 1,860, ta ƙwace tan 5.4 na miyagun ƙwayoyi a Kano
INEC ta yi ƙarin haske kan cire sunayen wasu ‘yantakarar gwamna a zaɓen 2027
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yanta'addan ISWAP fiye da 40 a Jihar Borno
Pantami ya bai wa INEC wa’adin kwana biyu ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe
'Yanbindiga sun kashe mutane 24 a sabbin hare-haren da suka kai a Nijeriya
Rahoton Bankin Duniya ya nuna ci gaba a sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya: Tinubu
Hukumar NDLEA ta sake kama wata tsohuwa mai shekara 83 kan zargin safarar miyagun kwayoyi
Kotu ta yi wa mutum uku ɗaurin shekara 21 kan satan yara a Nijeriya
'Yanta'adda na Lakurawa sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a jihar Kebbi a Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya za ta rage farashin man fetur tsawon kwanaki 30 a gidajen man NNPC
Bankin Duniya na hasashen tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da kashi 4.4% har zuwa 2028
An kuɓutar da ’yan NYSC 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Imo ta Nijeriya
’Yanbindiga sun kashe mutum 17 a Jihar Zamfara a Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 25 a Borno, sun ƙwato makamai
Nijeriya ta rage dogaro da kuɗaɗen shiga daga ɓangaren man fetur sosai – Tinubu
Shugaba Tinubu da Christopher Musa sun sake nazari kan tsarin tsaro da kariya na Nijeriya