Ƙasar Rasha ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine fiye da 1,000 cikin dare guda, inda ɗaruruwa daga cikinsu suka nufi yankin Moscow.
A safiyar Lahadi Ma'aikatar Tsaron Rasha ta bayyana cewa rundunonin tsaron sararin samaniya sun kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Ukraine guda 1,017 a yankuna fiye da goma sha biyu, ciki har da Moscow.
Magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin, ya ce fiye da jirage marasa matuƙa 500 ne suka nufi yankin babban birnin.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Max, wanda gwamnatin Rasha ke mara wa baya, Sobyanin ya ce na'urorin kariya daga hare-haren sama sun tare mafi yawansu tun suna nesa da birnin, yayin da suka kakkaɓo guda 105 a lokacin da suke tunkarar Moscow.
A ranar da ta gabata ma, Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matuƙa na Ukraine fiye da 1,200 a wani harin dare.
Ƙaruwar hare-hare ta sama
Rasha da Ukraine sun ƙara yawan hare-haren sama a cikin 'yan watannin nan, yayin da yaƙin ke shiga shekararsa ta biyar.
Ƙoƙarin Amurka na shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin bai haifar da wata yarjejeniya ba sai dai musayar fursunoni tsakanin ɓangarorin biyu.
A ranar Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya buƙaci Shugaban Rasha Vladimir Putin da ya “dakatar da duk wani nau'i na ta'addancin soja” kan ƙasashen Turai, a lokacin ganawarsu da suka yi a China a makon da ya gabata.
Trump, wanda ya bayyana Putin a matsayin abokinsa, ya ce yana ganin buƙatar tasa za ta iya taimakawa wajen cim ma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.
Shi ma wakilin Amurka, Jared Kushner, ya yi gargaɗin kada a ƙara tsananta rikicin, inda ya bayyana yaƙin a matsayin “yaƙin wakilci, inda Turai ke ɗaukar nauyin bayar da kuɗi da samar wa Ukraine makamai domin yaƙar Rasha”.














