Iran na fuskantar katsewar intanet a faɗin ƙasar, inda rahotanni ke nuna cewa an katse ayyukan sadarwa da amfani da wayar hannu.
"Bayanai na kai-tsaye sun nuna cewa a yanzu Iran tana cikin tsakiyar katsewar intanet a dukka faɗin ƙasar," in ji ƙungiyar sa ido kan intanet ta NetBlocks da ke Landan a wata sanara ta shafin X a ranar Alhamis.
Rahotannin kafofin watsa labarai sun ce an katse ayyukan wayar hannu jim kaɗan bayan rufe intanet, ko da yake hukumomin Iran ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
An ruwaito cewa katsewar ta biyo bayan gudanar da zanga-zanga a Iran tun daga ƙarshen Disamba, wanda ke da alaƙa da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da kuma ƙalubalen tattalin arziki da ke ci gaba da fuskantar ƙasar.
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon zanga-zangar da ake yi a Iran ya ƙaru zuwa 38, kamar yadda wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam da ta mayar da hankali kan Iran ta ruwaito a ranar Laraba.
Zanga-Zanga ta bazu a fadin kasar
Iran ta fuskanci zanga-zanga mai yawa tun daga watan da ya gabata, wadda aka fara daga ranar 28 ga Disamba a babbar kasuwar Tehran, saboda raguwar darajar kuɗin Iran da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.
Daga baya zanga-zangar ta bazu zuwa wasu birane da dama a faɗin ƙasar.
Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam da ke sa ido kan Iran ta ba da rahoton cewa masu zanga-zanga da dama sun mutu.
Hukumomin Iran ba su tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba ko kuma sun bayar da cikakkun bayanai game da waɗanda suka mutu ko suka jikkata.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran a ranar Laraba ta yi Allah wadai da "shisshigi a harkokin cikin gidan Iran" da Amurka ta yi a tsaka da zanga-zangar da ake yi a birane daban-daban.
Tehran ta jaddada a cikin wata sanarwa a shafin intanet na Ma'aikatar Harkokin Wajen cewa Amurka "tana da ƙiyayya ga al'ummar Iran" kuma ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin ɗabi'u da manufofin Amurka game da Iran.















