A karon farko a tarihin da aka rubuta, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai kwari a kusa da Hvalfjordur.
Wani mai sha'awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato ƙwari a Iceland), kamar yadda Hukumar Watsa Labarai ta Iceland ta faɗa a ranar Litinin.
An miƙa samfuran ga Cibiyar Tarihin Halitta ta Iceland don bincike, inda masanin ilimin halitta Matthias Alfredsson ya tabbatar da cewa lalle sauro ne.
An bayyana samfurin a matsayin Culiseta annulata, sauro mai jure sanyi da ake samu a arewacin Turai.
'Wataƙila ba zai tafi ba'
"Da alama sauron ba zai taɓa barin wajen ba," in ji Matthias. "Yana son ci gaba da samun ɗumi a lokacin hunturu a wurare masu inuwa kamar ɗakunan ajiya da gidajen dabbobi."
Duk da cewa sauro na zuwa kasar Iceland a wasu lokuta a cikin tayoyin jiragen sama, wannan shi ne karon farko da aka gano sun samu wajen zama a kasar Iceland.
Masana kimiyya sun daɗe suna hasashen cewa sauraye na iya samun kansu a Iceland.
Gano sauro a Iceland ya jaddada yadda yanayi da sauyin muhalli ke iya faɗaɗa kewayon nau'in ƙwari masu jure sanyi zuwa arewa fiye da kowane lokaci.