Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da auna matakan haɗin gwiwa da Malaysia a fannin tsaro a ƙarƙashin tsarin "kowa ya amfana", yayin da ƙasashen biyu ke neman faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban na dabaru, tattalin arziki, da kuma diflomasiyya.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa a Ankara tare da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim a ranar Laraba, Erdogan ya ce an gudanar da taron haɗin gwiwa na farko na manyan jami'ai - wanda aka amince da shi a lokacin ziyararsa a Kuala Lumpur a bara - wanda hakan ke nuna wani mataki na zahiri na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Erdogan ya kuma yi kira ga Malaysia da ta faɗaɗa zuba jarinta a Turkiyya, yana mai nuni da ƙaruwar damarmaki a fannin tsaro, ababen more rayuwa, da kuma manyan masana'antu.
Erdogan “Shugaba ne mai girma”
A nasa ɓangaren, Anwar ya yaba da fasahar ƙere-ƙere ta Turkiyya, yana mai yaba wa "ikon al'ummar Turkiyya da masana'antu a fannin kimiyya da fasaha," kuma ya ce Malaysia na kallon Turkiyya a matsayin abokiyar hulɗa mai muhimmanci a ci gaban da ke da alaƙa da ƙirƙire-ƙirƙire.
Anwar ya kuma gode wa Erdogan saboda abin da ya bayyana a matsayin "jagorancinsa mai jarumtaka ba kawai ga Turkiyya ba har ma ga duniya baki ɗaya, musamman ga duniyar Musulmi," wanda ke nuna kyakkyawan daidaiton siyasa tsakanin shugabannin biyu.
Baya ga tsaro da zuba hannun jari, Erdogan ya ce tattaunawar ta shafi ilimi, al'adu da alaƙar mutane, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙai na haɗin gwiwa na dogon lokaci.
"Mun kuma yi shawarwari kan batun bil’adama wanda ke samar da tushen abota da 'yan'uwantaka tsakanin Turkiyya da Malaysia," in ji Erdogan.
"Mun yanke shawarar ci gaba da ƙoƙarinmu a fannin ilimi, raya al'adu, da yawon buɗe ido, da kuma ɗaukar matakan da za su ƙarfafa tattaunawa tsakanin al'ummominmu," in ji shi.
An kuma tattauna batutuwan yanki da na duniya, inda ɓangarorin biyu suke da ra’ayi da matsaya iri guda.
"Musamman, za mu ci gaba da bin diddigin Gaza sosai," in ji Erdogan, yana mai jaddada damuwa game da rikicin yankin.
Shugaban Turkiyya ya ƙara da cewa Ankara ta bayar da muhimmanci ga hulɗa da abokanta na yankin da kuma ASEAN a ƙarƙashin shirinta na ‘Asia Anew’, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2019, kuma ta yaba da ƙoƙarin Anwar na taimaka wa wajen rage tashin hankali tsakanin Thailand da Cambodia.














