Yayin da ya rage watanni a fara Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, gwarzon ɗanwasan Brazil, Neymar ya amsa cewa zai iya yin ritaya a wannan shekarar.
Sai dai har yanzu yana da burin a saka shi cikin tawagar da za ta wakilci ƙasarsa a gasar kofin duniya. Kuma wannan ya sa yana ganin sai zuwa ƙarshen shekarar 2026 zai iya ajiye takalman ƙwallo.
Tsawon shekarunsa na wasa a tawagar Brazil da ma ƙungiyoyin da ya bugawa wasa a gida da Turai da Asiya, Neymar ya sha fama da raunukan da ke haddasa masa doguwar jinya.
Faɗi-tashi da har yanzu yake fama da ita shi ne ya sa ɗanwasan mai shekaru 34 ke ganin lokaci ya fara ƙarato masa na barin buga ƙwallon ƙafa kacokan.
Ko a Disambar da ta gabata, an yi wa Neymar tiyata a gwiwa, wadda da ma matsala ce da ta daɗe tana damun sa. Hasali ma ciwon ya taɓa hana shi buga ƙwallo tsawon shekara guda.
Yawan ƙwallo a Brazil
A yanzu dai Neymar yana buga wa ƙungiyar Santos ta Brazil, inda yake da kwantiragin da za ta kai ƙarshen shekara. A baya ya buga wa Barcelona ta Sifaniya, Paris Saint-Germain ta Faransa, da Al-Hilal ta Saudiyya.
Sai dai rabonsa da buga wa tawagar Brazil ta Selecao tun Oktoban 2023. A yanzu yana dakon jiran kocin ƙasar, Carlo Ancelotti ya fitar da zaɓin ‘yan-ƙwallon da za su buga masa gasar Kofin Duniya.
Tun sanda ya fara buga wa Brazil a 2010, Neymar ne ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihi, inda ya ci ƙwallo 79 a wasanni 128 . Rabon Brazil ɗaga kofin duniya tun a 2002.
Tawagar Brazil na da zaratan ‘yanwasa da za su iya buga mata, ciki har da Vinicius Junior na Real Madrid, da Raphinha na Barcelona, da Estevao na Chelsea. Wannan ya sa dole Neymar ya nuna cikakken kuzari don samun shiga tawagar.







