| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Shugaba Erdogan ya miƙa saƙon 'Barka da Azumi' ga ƙasarsa da duniyar Musulmai
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana fatan cewa watan mai albarka zai karfafa hadin kai da kawo albarka ga ‘yan adam.
Shugaba Erdogan ya miƙa saƙon 'Barka da Azumi' ga ƙasarsa da duniyar Musulmai
Shugaba Erdogan ya halarci taro da gwamnoni a fadar Shugaban Kasa da ke Ankara. / AA
19 Fabrairu 2026

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya miƙa sakonsa na watan Ramadan mai albarka, yana mai bayyana fatan cewa watan zai kawo albarka da hadin kai ga kasarsa, duniyar Musulmi da ma dukkan ‘yan adam baki daya.

Ya fitar da sakon fatan alherin a shafin sadarwa na Turkiyya na NSosyal, yana mai cewa watan mai albarka “zai kawo alherai ga kasarmu, duniyar Musulunci da dukkan bil’adam.”

Shugaban ya bayyana wannan lokaci a matsayin ‘Lokacin da ake bude kofofin Rahama” kuma ya yi addu’ar Allah Ya sa su zama ƙarfafa goyon baya.

Erdogan ya kuma yi addu’ar “wadannan kwanaki masu albarka za su karfafa hadin kanmu da zamanmu tare.”