Gwamnatin Nijar ta soke ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Nijar ɗin ce ta soke ayyukan ƙungiyoyin sakamakon rashin bin ƙa’idojin aiki musamman rashin gabatar da takardunsu na ayyuka a lokacin da gwamnatin ƙasar ke duba ayyukansu a tsakanin 14 zuwa 15 ga Nuwambar 2015 duk da sanar da su da aka yi game da hakan, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar.
A cikin fiye da ƙungiyoyi masu zaman kansu fiye da 3,000, ƙungiyoyi 1,684 na ƙasar ne kaɗai suka cika sharuɗa sai kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 125 ne suka cika sharuɗan.
A halin yanzu ƙungiyoyi 1,809 ne kawai suka cika sharuɗan da suka dace domin ci gaba da gudanar da ayyukansu a ƙasar.
Gwamnatin ta Nijar ta ce ta wallafa cikakkun sunayen duka ƙungiyoyin da suka cancanta su ci gaba da gudanar da ayyukansu a ƙasar a cikin takardun dokar da gwamnatin ƙasar ta yi.













