An kashe mutum 1,247 a Haiti tare da jikkata 710 daga watan Yuli zuwa Satumba, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya, yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan daba da bangaren jami’an tsaro, lamarin da ke tagayyara al'ummomi.
A cikin rahoton da ake fitarwa duk rubu’in shekara kan kasar ta Tsibirin Caribbean da aka wallafa a ranar Talata, Ofishin Haɗin Kan Majalisar Dinkin Duniya a Haiti (BINUH) ya kuma yi gargadi game da karuwar cin zarafin yara da yaduwar fyade.
Tashin hankalin 'yan daba ya mamaye babban birnin Port-au-Prince tun 2021 da kashe Shugaba Jovenel Moïse. A yanzu ‘yan daba ne ke iko da kashi 85 cikin 100 na birnin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
An tilasta wa ‘yan Haiti fiye da miliyan 1.3 yin kaura saboda wannan tashin hankali, abin da ya zama mafi girman ƙaura sakamakon rikicin siyasa a tarihin Haiti.
Yawancin mace-macen sun faru ne sakamakon ayyukan tsaro na gwamnati
Sashen Kare Hakkin Dan’Adam na BINUH ya gano nau'o'in masu ruwa da tsaki da dama cikin tashin hankali a rahoton, ciki har da 'yan daba masu makamai da kungiyoyin kare kai da fararen hula marasa tsari da hukumomin tsaron Haiti waɗanda ke gudanar da hare-haren ƙasa da na jiragen sama marasa matuka.
Duk da cewa an danganta kashi 30 cikin 100 na kisan da rikicin 'yan daba, rahoton ya nuna cewa yawancin mutuwar — kamar kashi 61 cikin 100 — sun faru ne sakamakon ayyukan rundunar tsaron Haiti.
Mace-macen sun faru ne a lokacin hare-haren kasa da na jiragen sama marasa matuka da kuma ta hanyar yin amfani da karfin iko fiye da kima, ciki har da kisan gaggawa.
Ƙarin kashi 9 cikin 100 na kisan an danganta su da kungiyoyin kare kai da gungun mutane masu hallaka jama’a.
Maza sun kasance kashi 83 cikin 100 na duk wadanda suka mutu, yayin da mata da yara suka kai kaso 14 cikin 100 da 3 cikin 100 bi da bi — adadin da suka yi daidai da abin da rahotannin MDD na baya suka nuna.
Cin zarafin yara
Rahoton ya jaddada safarar yara da amfani da su ta hannun 'yan bindiga a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin take hakkin dan’adam a Haiti.
A cewar bayanan hukuma, akalla yara 302 aka ɗauka aikin daba a 2024, duk da cewa MDD ta lura cewa adadin na gaske mai yiyuwa ya fi haka yawa.
Shaidu da Sashen Kare Hakkin Dan’Adam na BINUH ya tattara daga hukumomi da kungiyoyin agaji na duniya sun tabbatar da karuwar ɗaukar yara.
Duk da haka, MDD ta gargaɗi cewa rashin bayar da rahoto yana nan a matsayin babban cikas, saboda tsoron ramuwar gayya, tsangwama a al'umma da yawaitar rashin amincewa da 'yan sanda da hukumomin shari'a.
A sakamakon haka, kankanin adadin waɗanda abin ya shafa ne kaɗai ke fitowa su bayar da rahoto.
Rahoton ya kuma yi bayanin yaduwar fyade a yankunan da 'yan daba ke iko da su, musamman a matsayin fyaden taron dangi da ake aikatawa yayin kutse gidaje ko hare-hare a titi.
A wani misali daga watan Satumba, wata 'yar shekara 17 a Simon Pele, unguwa mai cunkoso a cikin gagarumin yankin talakawa na Cite Soleil kusa da Port-au-Prince, wasu ‘yan daba ne sun yi mata fyaden taron dangi ta hanyar nuna mata bakin bindiga bayan da suka kutsa gidanta.
A lardin Artibonite a tsakiyar Haiti, BINUH ta rubuta lokuta na cin zarafin yara da suka shafi ƙungiyar 'yan daba Kokorat San Ras, wadanda suka shafi akalla yara 27 masu shekaru 13 zuwa 17.















