Karancin ma'aikata a cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Amurka, tare da umurnin Hukumar Kula da Sufurin Sama ta Tarayyar Amurka (FAA) na rage adadin jirage da kashi huɗu a cikin 100 a manyan filayen jiragen sama 40, ya janyo soke tashi da saukar fiye da jirage 2,000 daga Juma'a zuwa Lahadi.
Ana kallon wannan soke-soken jiragen a matsayin mafi girma a sufurin jirage mafi girma a Amurka tun bayan da aka fara dakatar da gudanar da al’amuran gwamnati a ƙasar fiye da wata guda kenan.
Rage adadin jirage da FAA ta umurta ya fara da kashi huɗu a wannan karshen mako, kuma an tsara shi zai ƙaru zuwa kashi shida nan da 11 ga Nuwamba, kashi takwas nan da 13 ga Nuwamba, da kashi 10 nan da 14 ga Nuwamba.
Kamfanonin jiragen saman SkyWest, Southwest, da Envoy Air su ne kan gaba a waɗanda aka fi soke tashi da saukarsu yayin da United, Delta, da American Airlines ma suka samu jinkiri sosai, in ji FlightAware.
Kamfanonin jiragen sama dole ne su ƙara yawan raguwar jirage a hankali a cikin makon gobe, inda Sakataren Sufuri Sean Duffy ya yi gargaɗin cewa ragowar na iya kaiwa kashi 20 idan dakatarwar gwamnatin ta ci gaba.
Karuwar rage yawan jirage
A yayin da yake magana da Fox News, Duffy ya ɗora alhakin ƙarancin ma’aikatan ga dakatar da ayyukan gwamnati inda ya ce: 'Matsalar da muke da ita a gaskiya ita ce ba a biyan masu kula da zirga-zirgar jiragen sama albashi, kuma ana tilasta musu su yi wasu ayyukan na biyu, ko dai aikin gidan abinci ko kuma tuƙa motocin Uber maimakon su je su yi ayyukansu na kula da sufurin jirage.”
'Idan wannan dakatarwar ba ta kare cikin 'yan kwanaki ba, sakamakon haka shi ne ƙarin masu kula da sufuri ba za su zo aiki ba. Sannan za mu ci gaba da kimanta matsin lamba ga zirga-zriga jiragen sama mu yanke shawarar da watakila za mu iya komawa daga kaso 10 zuwa 15 ko kuma watakila 20,” in ji shi.
Dakatar da gudanar da al’amuran, wadda ta fara 1 ga Oktoba, ta jawo dakatar da biyan albashi ga ma'aikatan tarayya, ciki har da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama da jami'an Hukumar Tsaro ta Sufuri (TSA), waɗanda ke ci gaba da aiki ba tare da albashi ba.














