| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An fara jefa ƙuri’a a zaɓen Uganda bayan katse lntanet
Har ya zuwa lokcain hada labaran nan akwai wasu rumfunan zabe da ba a bude ba awanni bayan lokacin da aka tsara za a fara kada kuri’a a ranar Alhamis, inda ake sa ran masu jefa kuri’a miliyan 21.6 za su yi zabe.
An fara jefa ƙuri’a a zaɓen Uganda bayan katse lntanet
Wani mutum na jefa kuri'arsa a Kampala babban birnin Uganda. / AP
15 awanni baya

An fara kada kuri'a a ranar Alhamis a zaben shugaban kasa na Uganda duk da rufe intanet na tsawon kwanaki yayin da Shugaba Yoweri Museveni ke neman tsawaita mulkinsa na shekaru 40.

Jama'a sun taru kuma an yi dogayen layuka a wasu yankuna yayin da aka jinkirta bude rumfunan zabe kuma an ga ana isar da kayan zabe bayan lokacin bude rumfunan zaben da aka tsara da karfe 7 na safe.

Shugaba Yoweri Museveni, mai shekaru 81, yana fuskantar 'yan takara bakwai, ciki har da Robert Kyagulanyi, wani mawaki kuma dan siyasa wanda aka fi sani da Bobi Wine, wanda ke kira da a kawo sauyi a siyasa.

Masu jefa kuri'a za su kuma zabi 'yan majalisa sama da 500.

Kasar ta Gabashin Afirka mai mutane kusan miliyan 45 tana da masu jefa kuri'a miliyan 21.6 da suka yi rajista. Ana sa ran za a rufe kada kuri'a da karfe 4 na yamma agogon kasar tare da sa ran samun sakamako cikin awanni 48.

Gwamnati ta rufe intanet a ranar Talata na tsawon lokaci marar iyaka don hana yaduwar "labaran karya" da "tunzura tashin hankali".

Majalisar Dinkin Duniya ta kira rufewar "abin damuwa kwarai da gaske".

Rahotanni sun ce a babban birnin Kampala da birnin Jinja an samu jinkiri wajen fara jefa kuri’a.

"Babu wanda ke nan don ya gaya mana abin da ke faruwa," in ji Abuza Monica Christine, 'yar kasuwa mai shekaru 56 a tsakiyar Jinja, ta shaida wa AFP.

"Na'urorin tantance yanayin ba sa aiki don haka ba mu san abin da ke faruwa ba," in ji Katomgole Juma, wani mai sana'a mai shekaru 48 da ke jiran kaɗa ƙuri'a a tsakiyar Kampala.

Wani jami'in jam'iyya mai mulki ya shaida wa AFP cewa "Wasu na'urorin tantance yanayin ba sa aiki. Ban sani ba ko intanet ne. Ba mu sami wani bayani daga (hukumar zaɓe) ba".

'Yan sanda sun yi gargaɗin cewa zaɓen "ba hujja ba ce ta aikata laifuka" kuma sun tura sabbin "'yan sanda na musamman" da aka ɗauka aiki don tabbatar da doka da oda.