| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 18 daga hannun 'yanbindiga a gaɓar tekun Kamaru
Manjo Sokoya ya ce nan-take dakarun Birged ta 13 da ke aiki a Ikang suka bi sawun ‘yanfashin tekun, inda suka yi ta musayar wuta lamarin da ya sa ɗaya daga cikin kwalekwalensu ya kife.
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 18 daga hannun 'yanbindiga a gaɓar tekun Kamaru
An kama 'yanfashin teku a yankin ruwan Kamaru / Nigerian army
12 Janairu 2026

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta na Birged ta 13 sun yi nasarar ceto mutum 18, ciki har da ƙananan yara biyu, bayan ‘yanbindiga sun yi garkuwa da su a kwalekwale yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kamaru.

Wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun Birged ta 13 Manjo Yemi Sokoya ya fitar ranar Litinin ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadin da ta wuce.

Ya ƙara da cewa wasu da ake zargi ‘yanfashin teku ne a cikin kwalekwale guda biyu masu gudun tsiya da kwalekwale na katako sun yi garkuwa da wani kwalekwale da ke ɗauke da fasinjoji 18 da ke kan hanya daga Nijeriya zuwa Kamaru.

‘Yanfashin sun sace mutanen ne a gaɓar tekun da ake kamun kifi mai suna Kombo Fishing Port da ke ɓanagren Kamaru.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Nijeriya sun ciro gawarwaki 27 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe

Manjo Sokoya ya ce nan-take dakarun Birged ta 13 da ke aiki a Ikang suka bi sawun ‘yanfashin tekun, inda suka yi ta musayar wuta da su lamarin da ya sa ɗaya daga cikin kwalekwalensu ya kife.

Daga nan ne ‘yanfashin tekun suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su inda suka tsere cikin wani daji da ke kusa, in ji sanarwar tana mai ƙari da cewa “an ceto dukkan fasinjojin ba tare da samun ko da ƙwarzane ba.”

Kwamandan Birged 13 ta Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya Janar PO Alimikhena ya yaba wa dakarun da suka yi gaggawar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.