Ministan ilimi na ƙasar Mali Amadou Sy Savane ya sanar a ranar Lahadi cewa, za a rufe makarantu a duk faɗin ƙasar na tsawon makonni biyu saboda ƙarancin man fetur da ake fama da shi.
Amadou Sy Savane ya shaida wa gidan rediyon gwamnati na ORTM cewa dukkan cibiyoyin ilimi a faɗin ƙasar ta Yammacin Afirka za su dakatar da ayyukansu daga 27 ga Oktoba zuwa 9 ga Nuwamba saboda ƙarancin fetur.
Savane ya ce an shirya sake buɗe makarantu a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Tsawon makonni dai, Mali ta fuskanci matsalar ƙarancin man fetur sakamakon toshe hanyoyin wucewar manyan motoci masu dakon mai da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke yi, musamman hanyar da ke zuwa babban birnin ƙasar Bamako.
An fuskancin dogayen layukan motoci a gidajen mai a sassan ƙasar, yayin da ayyukan motocin sufuri da babura suka tsaya cak, lamarin da ya sa titunan Bamako da ke suka su batse saboda cunkoso suka yi tsit.
Kazalika, an tilasta wa cibiyoyin ilimi na manyan makarantu a babban birnin dakatar da shiga azuzuwa saboda gazawar dalibai da malamai wajen isa jami'o'in sakamakon ƙarancin man fetur.
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Bamako ya sanar a ranar 24 ga Oktoba cewa ƙananan ma'aikatan diflomasiyya na ƙasar da iyalansu za su bar Mali a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin mai ga kuma matsalolin tsaro da ke ɗaɗa ƙaruwa.
A ranar Juma'a, ofishin jakadancin ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullun ko na gaggawa a wajen Bamako ba, kana ya yi ƙari da cewa a ci gaba da bibiyar shawarwarin tafiye-tafiye a Mali








