Dakarun RSF sun kashe mata 300 kuma sun yi wa wasu 25 fyaɗe a cikin kwanaki biyu na farko da suka shiga Al Fasher babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, in ji wata Ministar Sudan.
“RSF sun kashe mata 300 a cikin kwanaki biyu na farko da suka shiga Al Fasher,” in ji Ministar Walwala da Jin Daɗi Salma Ishaq ga kamfanin Anadolu.
Ta bayyana cewa mata a Al Fasher sun fuskanci “cin zarafi ta hanyar lalata, tashin hankali, da azabtarwa” kafin a kashe su.
“Dukkan mata a cikin birnin suna fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da kisa. Babu wata mace da ke da kariya, har ma da yara,” in ji ministar, tana mai nuna cewa an tabbatar da fyade har guda 25.
“Akwai rahotanni na ‘yan jarida mata da aka yi wa fyaɗe, kuma an bayyana waɗannan laifuka,” kamar yadda ta ƙara da cewa.
“An yi lalata da ‘ya’ya mata har a gaban iyayensu, waɗanda daga baya aka kashe su. Kowa ya ga waɗannan abubuwan a cikin bidiyo,” in ji ministar.
“Duk wanda ya fita daga Al Fasher zuwa Tawila (a Darfur ta Arewa) yana cikin haɗari, saboda hanyar tsakanin biranen biyu ta zama ‘hanyar mutuwa’,” kamar yadda Salma Ishaq ta bayyana, tana mai nuna cin zarafin a gangar jiki da kalaman wariyar launin fata da ake yi wa mata.
“RSF suna amfani da cin mutunci da fyade a matsayin makami kan mata da ke tserewa daga Al Fasher.”
Ministar ta ce har yanzu akwai iyalai a Al Fasher da ke fuskantar azabtarwa, cin mutunci, da cin zarafi ta hanyar lalata.
“Abin da ya faru a Al Fasher wani tsari ne na kisan kare dangi, babban laifi wanda kowa ya zama mai hannu a ciki ta hanyar shiru,” kamar yadda ta ƙara da cewa.
Laifukan RSF
Ishaq ta ce laifukan RSF a Al Fasher suna kama da kisan kare-dangi da ya faru a Geneina, babban birnin Darfur ta Yamma a 2023.
A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya a watan Janairun 2024, tsakanin mutane 10,000 zuwa 15,000 aka kashe a Geneina, ciki har da gwamnan jihar, a rikicin ƙabilanci da RSF da ƙungiyoyin ‘yan tawaye suka yi.
“Tabbas, abin da ya faru a Geneina ba a adana shi ba kamar na Al Fasher ba. Bidiyon da RSF suka dauka a Geneina ba su kai yawan na Al Fasher ba,” in ji Ishaq.
Ministar ta jaddada cewa rubuta laifukan RSF ya zama “wani bangare na makamin kungiyar ta ‘yan tawaye don samun nasara kan abokan gabar su.”
“Jin dadin kisa kansa yana ba su wata irin jin nasara. A fannin tunani, yana wakiltar wata cutar nasara. Maganar ita ce iko, kuma iko ya kasance babban makami ga RSF,” kamar yadda ta kara da cewa.
“Idan RSF suka ci gaba da kasancewa a Al Fasher, za su hallaka duk wani mutum a Darfur. Wannan tsari ne na kisan kare-dangi, kuma kowa ya zama mai hannu ta hanyar shiru,” kamar yadda ministar ta yi gargadi.
Ta sake nanata cewa shiru na al’ummar duniya zai kara karfin gwiwar RSF don aikata karin laifuka a Al Fasher da duka fadin kasar.
Tallafin jin kai
Game da tallafin jin kai a Al Fasher, Ishaq ta ce tallafin da aka kawo Tawila ta hannun wasu ƙungiyoyi bai isa don biyan buƙatun dubban iyalai da suka rasa matsugunansu a birnin ba.
Ta nuna cewa hukumomin gwamnati ba za su iya shiga yankin ba, saboda hakan zai jefa rayukan fararen-hula da ma’aikatan jin kai cikin haɗari.
A ranar 26 ga Oktoba, RSF sun karbe iko da Al Fasher kuma sun aikata “kisan ƙare-dangi” kan fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na ƙasa da ƙasa, tare da gargaɗin cewa harin na iya kara raba Sudan ta fuskar yanki.
A ranar Laraba, shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo (Hemetti) ya amince cewa “an samu cin zarafi” daga dakarunsa a Al Fasher, yana mai cewa an kafa kwamitocin bincike.












