An ji ƙarar fashewar bamabamai, tare da ƙarar jiragen sama a Caracas, babban birnin Venezuela da misalin ƙarfe 2:00 na dare (0600 GMT) ranar Asabar, kamar yadda wani ɗanjarida na kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
An ji waɗannan fashe-fashe ne bayan shugaban Amurka Donald Trump, ya sha alwashin kai hare-hare ta ƙasa a Venezuela. Tuni ya tura wata tawagar sojojin ruwa zuwa ƙasar wadda ke yankin Caribbea.
An ci gaba da jin ƙarar fashewar bamabamai da misalin ƙarfe 2:15 na dare, ko da yake ba a san takamaimai inda aka ji ƙarar ba.
Ranar Litinin Trump ya ce Amurka ta kai hari kan wani wani wurin ajiye jiragen ruwa inda ta lalata jiragen da ta yi zargin cewa na masu safarar miyagun ƙwayoyi ne ‘yan ƙasar Venezuela.
Trump bai bayyana jami’an da suka kai harin ba - sojoji ko jami’an hukumar leƙen asiri ta CIA - sannan bai faɗi wurin da aka kai harin ba, inda ya ce an kai shi ne “a gaɓar ruwa."
Wanna shi ne hari na farko da aka sani an kai a cikin ƙasar Venezuela.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya bayar da umarni ga duka ‘yan ƙasarsa su fito domin kare ƙasarsu, sanna ya zargi Amurka da mamaya tare da neman ƙasashen duniya su yi Allah wadai da wannan hari.












