Gwamnatin Sudan ta koma gudanar da ayyuka a hukumance a birnin Khartoum a ranar Lahadi, karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙin da aka fara dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) a watan Afrilun 2023, in ji Firaminista Kamel Idris.
Yayin da yake jawabi ga taron jama'a bayan isarsa daga Port Sudan, inda gwamnati ta kasance tana gudanar da aiki a matsayin babban birni na wucin-gadi tun lokacin rikicin, Idris ya bayyana wannan dawowa a matsayin muhimmin juyi ga ƙasar.
"A yau mun dawo, kuma tare da mu gwamnati mai cike da fata ta dawo zuwa babban birnin ƙasa," in ji shi. "Muna alkawarin inganta ayyuka da rayuwa mafi kyau ga mutanen mu."
Idris ya yi alkawarin ɗaga matakin kiwon lafiya da ilimi, sake gina asibitoci da gyara makarantu da jami'o'i, tare da ba da muhimmanci musamman ga Jami'ar Khartoum. Har ila yau ya yi alƙawarin inganta tsaro da yanayin rayuwa ga 'yan ƙasa.
‘‘Shekarar zaman lafiya’’
Firaministan ya ce gwamnati ta miƙa kasafin shekarar 2026 ba tare da ƙara nauyi na kuɗi ga jama'a ba, yana mai cewa gwamnati na da burin rage hauhawar farashin kayayyaki da kaso 70 cikin 100.
A cewar sabbin bayanan hukuma da aka fitar a watan Nuwamba, hauhawar farashin ya kai kaso 74.2 cikin 100.
Idris ya ce kasafin kuɗin na kuma nufin ƙara haɓakar girman tattalin arzikin ƙasa (GDP) zuwa kashi 10 da kuma daƙile farashin musayar canji a kasuwannin bayan fage a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tattalin arziƙi.
Ya bayyana wannan shekarar a matsayin "shekara ta zaman lafiya," yana kiran ta "zaman lafiya na jarumai masu nasara."
Mummunan yaƙi
A ranar 21 ga Mayu, Rundunar Sojin Sudan ta sanar da sake karɓar cikakken iko a kan Khartoum, inda ta bayyana babban birnin ‘ya ‘yantu daga RSF bayan fafatawa a yankin Salha a kudu na birnin.
A watan Yulin da ya gabata, Shugaban Majalisar Mulkin Wucin-Gadi, Abdel Fattah al-Burhan, ya fitar da umurni na kafa kwamitin ƙasa don shirya Khartoum domin ma’aikatun gwamnati su yi gaggawar komawa can aiki da mazauna.
Daga cikin jihohi 18 na Sudan, RSF na kula da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur a yamma, sai dai wasu sassan arewa na Arewacin Darfur da ke ƙarƙashin ikon sojoji. A gefe guda, sojoji suna riƙe da mafi yawan sassan sauran jihohi 13 a kudu, arewa, gabas, da tsakiya, ciki har da babban birnin Khartoum.







