| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Ma'aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a wasu unguwannin Aleppo
Ma’aikatar tsaron Syria ta ce ‘yan bindiga suna da zuwa ƙarfe 9 na safe su bar unguwannin da ake rikici da su.
Ma'aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a wasu unguwannin Aleppo
Hukumomin Syria sun sanar da tsagaita wuta a Aleppo bayan aika jami’an tsaro na cikin gida zuwa wuraren da ake rikici / AA
15 awanni baya

Ma’aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a wasu unguwanni na arewacin birnin Aleppo, inda ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin kawo karshen ayyukan soja a wuraren.

A cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Syria (SANA) ya wallafa, tsagaita wutar ta fara aiki da misalin karfe 3:00 na asuba agogon cikin gida ranar Juma’a a unguwannin Ashrafieh, Sheikh Maqsoud da Bani Zeid, bayan da hukumomi suka ce an samu cikakken iko a wadannan gundumomi.

Ma’aikatar ta ce an bai wa ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai wa’adin zuwa karfe 9:00 na safiyar ranar Juma’a su fice daga unguwannin, domin a kawo ƙarshen yanayin soja gaba daya.

Wannan sanarwa ta biyo bayan bayanin da Ma’aikatar Cikin Gida ta fitar kan cewa jami’an tsaron cikin gida na Syria sun fara shiga unguwar Ashrafieh, bayan ficewar ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG daga yankin.

Hukumomi sun ce wannan shigar ta biyo bayan sauya sheƙa da yawancin mambobin YPG suka yi daga Sheikh Maqsoud da Ashrafieh, yayin da wasu kuma suka tsere daga yankunan.

Sojojin Syria sun kuma kai hare-haren bama-bamai masu tsanani a kan wuraren YPG a Aleppo, inda hukumomi suka ce hakan martani ne ga hare-haren da kungiyar ta kai, wadanda suka kashe akalla fararen hula tara tare da jikkata daruruwa.

A ranar 10 ga Maris ɗin 2025, fadar shugaban kasar Syria ta sanar da rattaba hannu kan wata yarjejeniya da nufin shigar da SDF cikin cibiyoyin gwamnati, tare da jaddada hadin kan yankin Syria da kuma kin amincewa da duk wani yunkurin rarrabuwar kasa.

Jami’ai sun ce kungiyar ta’addanci ta YPG ba ta dauki matakai masu ma’ana ba wajen aiwatar da sharuddan yarjejeniyar a watannin da suka biyo baya.

Gwamnati ta kara kaimi wajen kokarin dawo da kuma tabbatar da tsaro a fadin kasar tun bayan kifar da mulkin Bashar al-Assad a ranar 8 ga Disamban 2024, bayan shekaru 24 yana mulki.