Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta iya kai ƙarin hare-hare a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar, duk da cewa hukumomin Nijeriya sun musanta kashe Kiristoci.
Trump ya yi wannan barazana ce a wata hira da jaridar The New York Times ta wallafa ranar Alhamis.
A ƙarshen watan Disamba ne shugaban Amurka ya sanar da kai hari kan waɗanda ya bayyana a matsayin 'yanta'addar Daesh a arewa maso-yammacin Nijeriya inda aka “kashe 'yan ta'addan ISIS da dama”.
Nijeriya ta ce harin na "haɗin gwiwa ne" da aka kai kan “‘yanta'adda,” kuma ba shi da "alaƙa da wani addini."
"Ba na so na kai hari fiye da sau ɗaya ... Amma idan suka ci gaba da kashe Kiristoci, za mu kai hare-hare da yawa," in ji Trump.

Da aka tambaye shi game da kalaman mai ba shi shawara kan Afirka, wanda ya ce 'yanta'addar Daesh da Boko Haram suna kashe Musulmai fiye da Kiristoci, Trump ya amsa: "Ina tsammanin ana kashe Musulmai a Nijeriya. Amma galibi Kiristoci aka fi kashewa."
Ci gaba da kai farmakai
Adadin al’ummar Nijeriya ya zarta miliyan 230 - kuma Musulmai da Kiristoci suna kankankan a yawan jama’a - inda Musulmai suka fi yawa a arewacin ƙasar yayin da Kiristoci suka fi yawa a kudanci.
Nijeriya na fama da rashin tsaro a sassa daban-daban, ciki har dahare-haren ‘yanta’adda da masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa da kuma ‘yan a-aware na IPO, amma ta musanta cewa Kiristoci na fuskantar tsangwama.
Hukumomin Nijeriya sun bayyana cewa 'yanta’ada suna kashe Musulmai da Kiristoci ba tare da nuna bambanci ba.
Ministan harkokin wajen ƙasar Yusuf Tuggar kwanan baya ya ce ana ci gaba da yaƙi da ta’addaci kuma ya jaddada cewa Nijeriya ta samar da bayanan sirri game da harin da Amurka ta kai Sokoto, wanda ya bayyana a matsayin na haɗin gwiwa da Washington.
“Bisa yin la’akari ga ayyukan ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyoyin fahimtar juna na aiki tare, wannan haɗin gwiwa ya haɗa da musayar bayanan sirri, dabarun gudanar da ayyuka, da sauran taimakon juna da suka yi daidai da dokokin ƙasa da ƙasa na girmama ikon juna da tabbatar da aniyar bai-ɗaya ta samar da tsaro a duniya,” in ji wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar.











