| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Guinea-Bissau ta haramta taron manema labarai 'ba tare da izini ba' domin guje wa tashin hankali
Gwamnatin mulkin sojin Guinea-Bissau wadda ta yi juyin mulki a Nuwambar bara ta ce duk wata ƙungiya ko wani mutum da ya saɓa dokar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta tsara za a yi masa hukunci mai tsanani, daidai da yadda doka ta tanada
Guinea-Bissau ta haramta taron manema labarai 'ba tare da izini ba' domin guje wa tashin hankali
Shugaban rikon kwarya na Guinea-Bissau, Manjo-Janar Horta Inta-a, ya hau mulki a Nuwambar 2025. / Reuters
kwana ɗaya baya

Gwamnatin Guinea-Bissau a ranar Jumma'a ta sanar da haramta dukkan tarurrukan manema labarai, kimanin makonni shida bayan da gwamnatin ƙasar ta karbi iko a wani juyin mulki bayan zabe.

Bayan korar shugaban Umaro Sissoco Embalo a ranar 26 ga Nuwamba, nan take bayan zaben shugaban kasa, sojoji suka dakatar da tsarin zabe suka kuma bayyana cewa za su karɓi ragamar jagorancin ƙasar da ke yammacin Afirka na tsawon shekara guda.

A ranar Jumma'a, Majalisar Ƙoli ta Soji, wadda ita ce hukumar mulki da ke mulkin ƙasar, ta bayyana a wata sanarwa kan cewa 'wasu mutane da kungiyoyin kabilu, musamman 'yan siyasa, sun shirya tarurruka a asirce inda suka yi amfani da su wajen tada tarzoma da rashin biyayya, har da take kundin tsarin mulki na wucin-gadi na kasar.'

An wallafa kundin a farkon Disamba kuma yana da nufin a samar da tsarin doka ga ƙasar a ƙarƙashin mulkin soja.

Za a yi mummunan hukunci ga masu saɓa doka

Babban Hafsan Sojoji ya ce 'a takamaimai an haramta gudanar da duk wani taron manema labarai ko sanarwar jama'a da ba a da izini ba waɗanda za su iya kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kai na al'umma.'

'Duk wani mutum ko kungiya da ta kalubalanci dokar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta tsara za a yi masa hukunci mai tsanani, daidai da yadda doka ta tanada,' in ji sanarwar.

Bayan kifar da gwamnatin Embalo, gwamnatin soja a farko ta zargi manyan masu safarar miyagun kwayoyi da yin shiri don jefa kasar cikin hargitsi, kasar da ta yi ƙaurin suna wurin safarar hodar ibilis.

Amma a farkon Disamba, hukumomi sun ce maimakon haka kasar na fuskantar wani mawuyacin hali na siyasa a sakamakon kada kuri'a 'wanda zai iya rikidewa zuwa yaki na cikin gida da ke dauke da bangaranci na kabilanci.'

Kafin juyin mulkin Nuwamba, an gudanar da juyin mulki a Guinea-Bissau sau huɗu da kuma jerin yunkurin tashe-tashen hankula tun bayan samun 'yanci kai daga Portugal a 1974.