Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan manyan shugabanni uku na rundunar Rapid Support Forces (RSF) ta Sudan a wannan makon, bisa zargin aikata laifukan yaƙi da taken haƙƙin bil’adama a yayin yi wa birnin Al Fasher ƙawanya na tsawon watanni 18 a yankin Arewacin Darfur.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da masu bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi gargaɗin cewa ayyukan da dakarun RSF suka aikata a lokacin ƙwace birnin a ƙarshen watan Oktoba na ɗauke da “alamomin kisan-kare dangi,” lamarin da ke nuna buƙatar ƙara tsanantar sa ido na ƙasa da ƙasa kan ta’asar da ake zargin an aikata a yammacin Sudan.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar a ranar Alhamis, ta ce mutanen da aka ƙaƙaba wa takunkumin mambobi ne na RSF “waɗanda dakarunsu suka aikata kisan ƙare-dangi da aikata laifukan yaƙi da kuma manyan take-taken haƙƙin bil’adama a Sudan.”
Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka, ta hannun Ofishinta na Kula da Kadarorin Ƙasashen Waje, ta ce kwamandojin ukun sun taka muhimmiyar rawa a tsawon lokacin da aka ɗauka na yi wa birnin Al Fasher ƙawanya, wadda ta zo ƙarshe a watan Oktoba bayan dakarun RSF sun ƙwace iko da birnin bayan watanni na ƙawanya da luguden wuta.
A cewar Ma’aikatar Baitulmalin Amurka, mayaƙan RSF sun aikata kashe-kashen da aka yi bisa ƙabilanci, azabtarwa, amfani da yunwa a matsayin makami, da kuma fyaɗe da cin zarafin mata a yayin hare-harensu.
Takunkumin ya haɗa da ƙwace duk wata kadara da suke da ita a Amurka ko a ƙarƙashin ikon Amurka, tare da haramta wa ‘yan ƙasa ko kamfanonin Amurka yin mu’amala da waɗannan kwamandoji. Haka kuma, duk wata hukuma ko kamfani da suke mallakar kashi 50 cikin 100 ko fiye na hannun jari a cikinsa zai fuskanci irin waɗannan takunkumai.
Abu Lulu: Zargin kashe-kashen jama’a
Daga cikin waɗanda aka ƙaƙaba wa takunkumi akwai Al-Fateh Abdullah Idris Adam, wanda aka fi sani da Abu Lulu.
Jami’an Amurka sun zarge shi da aikata ta’asa da kansa a lokacin yi wa Al Fasher ƙawanya, tare da ɗaukar bidiyon kansa yana kashe fararen-hula marasa makami.
Ma’aikatar Baitulmalin ta ce Abu Lulu na yi wa sojojin Sudan da aka kama tambayoyi, yana tilasta musu bayyana ƙabilarsu tare da rera taken goyon bayan RSF kafin ya harbe su.
Haka kuma, ta ambaci rawar da ake zargin ya taka a kisan da aka yi wa fursunoni a matatar man Al-Jaili da ke arewacin Khartoum a watan Maris ɗin 2024.
Bidiyoyi da suka yaɗu a lokacin faɗace-faɗacen Darfur sun nuna Abu Lulu yana murnar kashe-kashen da aka yi a fagen daga tare da iƙirarin kashe ɗaruruwan mutane.
A ranar 30 ga Oktoban bara, RSF ta sanar da cewa ta tsare shi domin gudanar da bincike kan laifukan da ake zargin ya aikata a Al Fasher bayan ƙwace birnin.








