Zanga-zangar kan karuwar matsalolin tattalin arziki a Iran ta rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aƙalla mutane shida suka mutu a arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a sassan yammacin ƙasar, abin da ya zama farkon mutuwar da aka ruwaito tun bayan da zanga-zangar ta ɓarke a farkon makon nan.
Zanga-zangar ta ɓarke a ranar Lahadi a Tehran, inda 'yan kasuwa suka gudanar da yajin aiki don nuna rashin jin daɗi kan hauhawar farashi da tsawaitar matsin tattalin arziki. Tun daga lokacin, zanga-zangar ta yaɗu zuwa wasu birane da dama, inda ɗalibai da wasu ƙungiyoyi suka shiga.
A ranar Alhamis, kamfanin dillancin labarai na Fars na Iran ya ruwaito cewa mutane biyu sun mutu a arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a garin Lordegan, a lardin Chaharmahal and Bakhtiari, mutane uku a Azna, a lardin Lorestan.
‘Yan sanda sun mayar da martani da hayaki mai sa hawaye, kuma an kama wasu mutane da hukumomi suka bayyana a matsayin 'jagororin masu tarzoma', in ji Fars, wanda ya ƙara da cewa an yi wa gine-gine da dama mummunar ɓarna.
Tun da farko a ranar Alhamis, gidan talabijin ɗin gwamnati ya ruwaito cewa an kashe wani mamba na jami'an tsaron sa kai na Iran cikin dare yayin rikici a garin Kouhdasht a yammacin ƙasar.
An bayyana mamacin a matsayin wani mamba na ƙungiyar Basij mai shekara 21 , wata kungiyar sa-kai da Khomeini ya kafa jim kaɗan bayan juyin juya hali na 1979.
Said Pourali, mataimakin gwamnan lardin Lorestan, ya ce jami'an 'yan sanda 13 da mambobin Basij sun ji rauni sakamakon jifa-da-duwatsu yayin zanga-zangar a Kouhdasht.
Tashin hankali na karuwa a Iran
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi ƙoƙarin kwantar da rikicin, inda ya amince da "halattattun bukatun" masu zanga-zangar, yana mai kira ga gwamnatinsa da ta dauki matakai wajen shawo kan wahalhalun tattalin arziki.
A lokaci guda kuma, hukumomi sun yi alkawarin mayar da martani mai ƙarfi ga duk wani tashin hankali, suna gargadi kan abin da suke kiran ƙoƙarin amfani da koke-koken tattalin arziki don haifar da rashin kwanciyar hankali.
Babban mai shigar da kara na Iran ya ce zanga-zangar kan tattalin arziki ta lumana tana da halastacciya ce, amma ya yi alkawarin 'mayar da ƙaƙƙarfar martani' ga ayyukan rashin tsaro ko lalata dukiyar jama'a.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, mai nasaba da gwamnati, ya ruwaito cewa an kama mutane bakwai da ake zargin suna da alaƙa da kungiyoyin da suke kira 'maƙiyan Iran' da ke Amurka da Turai, tare da zarginsu da ƙoƙarin juya zanga-zangar zuwa tashin hankali.
Darajar kuɗin Iran ya rasa fiye da kashi ɗaya cikin uku na darajarsa a kan dalar Amurka a cikin shekarar da ta gabata, yayin da hauhawar farashi ta rage ƙarfin sayayya tsawon shekaru.












