| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An daƙile yunƙurin kifar da gwamnatin Traore na Burkina Faso Traore: minista
Ministan tsaro Burkina Faso ya zargi tsohon shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba da kitsa yuƙurin juyin mulkin.
An daƙile yunƙurin kifar da gwamnatin Traore na Burkina Faso Traore: minista
Kyaftin Ibrahim Traoré na Burkina Faso ya halarci taron ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES) a Bamako, Mali ranar 23 ga Disamban 2025. / Reuters
7 Janairu 2026

Gwamnatin Burkina Faso ta zargi tsohon shugaban ƙasar Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba da kitsa yunƙurin kifar da mulkin Shugaba Ibrahim Traore wanda bai yi nasara ba.

Ministan tsaron ƙasar Mahamadou Sana ranar Talata da daddare ya sanar a gidan talbijin na ƙasar RTB cewa an daƙile yunkurin juyin mulkin wanda aka kitsa ranar Asabar da ta gabata, inda ya “gode wa jami’an leƙen asiri bisa ƙwarewarsu.”

Ya ƙara da cewa an shirya kashe manyan jami’an gwamnati na soji da fararen-hula, tare da kashe Kyaftin Traore ta hanyar harbe shi daga kurkusa ko kuma sanya bamabamai a gidansa.

Masu AlakaTRT Afrika - Ibrahim Traore: Abin da ya sa shugaban Burkina Faso ke jan hankalin duniya

“Bayan haka, an kitsa lalata sansanin jirage marasa matuƙa tare da aiko sojojin ƙasa daga ƙasashen waje,” in ji shi.

Sana ya ce hukumomi za su fitar da sunan babban wanda ake zargi da kitsa yunƙurin juyin mulki ne saboda dalilai na tsaro, inda ya bayyana Damiba a matsayin wanda ake zargi, yana mai cewa ya tsara kifar da gwamnati tare da samar da kuɗaɗen aiwatar da shirin da kuma ɗaukar hayar sojoji da fararen-hula da za su yi aikin.

Ya ƙara da cewa an bai wa sojojin da za su yi juyin mulkin damar ɗauko wasu dakaru, inda su kuma fararen-hula za su mayar da hankali wajen neman goyon bayan ‘yan ƙasar domin kifar da gwamnati.

“Za mu bai wa ‘yanjarida bidiyoyi na mutanen da suka kitsa juyin mulkin inda suke bayyana rawar da kowanensu ya taka,” a cewarsa.