Kamfanin matatar mai na Dangote ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta waɗanda ke nuna cewa yana shirin dakatar da ayyukansa don gyare-gyare, yana mai bayyana hakan a matsayin karya da kuma yaudarar jama’a.
A sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Litinin, ya ce matatar na ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da tsaiko ba, kana ya ba da tabbacin samar da man Premium Motor Spirit (PMS).
A cewar Dangote, matatar tana da ƙarfin samar da lita miliyan 40 zuwa 50 na mai a kowace rana cikin watan Janairu da Fabrairu, bisa ga buƙatar kasuwa.

Ya kuma bayyana cewa a ranar 4 ga Janairu, matatar ta samar da lita miliyan 50 ta PMS sannan ta fitar da lita miliyan 48, kazalika ya bayyana cewa kayayyakin da ake da su yanzu sun za su isa kwanaki 20 ana amfani da su a kasa.
Matatar ta fayyace cewa gyare-gyaren da ake yi a kan kari a sassan matatar ba zai dakatar da ayyukan samar da mai na kamfanin gaba ɗaya ba.
Matatar ta ce tun daga ranar 16 ga Disamba, 2025, ta samar da lita miliyan 31 zuwa 48 na PMS a duk rana, daidai da yawan buƙatun kasuwa.
Kazalika ta tabbatar da cewa tana ci gaba da sayar da PMS akan farashin da bai wuce N699 kan kowace lita ga ‘yan kasuwa da masu amfani da yawa.
"Ana shawartar masu ruwa da tsaki da jama'a da su yi watsi da rahotannin karya, sannan a ci gaba da taka tsantsan game da magudin farashi, ‘‘ a cewar sanarwar matatar
Sanarwar ta kuma kara da cewa a dogara kan bayanai da aka tabbatar daga majiyoyi masu inganci.








