GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa gabanin babban taron MDD
Ƙasashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka shiga cikin jerin ƙasashen Yamma da ke goyon bayan samun 'yancin Falasɗinu yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba.
Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa gabanin babban taron MDD
Wannan na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza / Reuters
5 awanni baya

Ƙasashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka shiga cikin jerin ƙasashen Yamma da ke goyon bayan samun 'yancin Falasɗinu yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba.

Birtaniya

“A sakamakon wannan bala'in da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, muna ɗaukar mataki don tabbatar da yiwuwar zaman lafiya da mafitar two-state solution {wato ƙasashe biyu wadda kowace ke cin gashin kanta},” in ji Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a cikin wani bidiyo da ya fitar.

Ya ce wannan yana nufin samun Isra'ila mai aminci da tsaro tare da Falasdinu mai ɗorewa, inda ya ƙara da cewa: “A halin yanzu, ba mu da ko ɗaya.”

A watan Yuli, Firaministan ya ce Birtaniya za ta amince da Falasɗinu a watan Satumba idan gwamnatin Isra'ila ba ta ɗauki matakan da suka dace ba.

A gefe guda, gwamnatin Isra'ila ta bayyana matakin Birtaniya a matsayin “abin dariya” kafin sanarwar ta fito.

Kafin sanarwar, mataimakin Firaminista David Lammy ya shaida wa BBC cewa “yanzu lokaci ne da ya dace mu tsaya tsayin daka don mafitaf two-state solution.”

Canada

Firaministan Canada Mark Carney, a ranar Lahadi ya sanar da cewa ƙasarsa ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, tare da yin alƙawarin haɗin kai don gina zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra'ila.

“Canada ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa kuma za ta bayar da haɗin kai wajen gina makoma mai zaman lafiya ga Falasɗinu da Isra'ila,” in ji Carney a shafin sada zumunta na X kafin taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sanarwar ta biyo bayan furucin Canada a baya na niyyar amincewa da Falasɗinu a lokacin zaman taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a watan Satumba 2025.

Australiya

Ita ma Australiya ta bi sahun takwarorinta wato Canada da Birtaniya wurin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa wanda wannan wani yunkuri ne na farfaɗo da mafita ta two-state solution wanda zai fara da tsagaita wuta a Gaza da sakin waɗanda aka kama a can, in ji Firaminista Anthony Albanese a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa tare da Ministan Harkokin Waje Penny Wong.

A baya, Faransa, Luxembourg, da Malta sun sanar da shirin su na amincewa da Falasɗinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.