Majalisar Dokokin Amurka ta gabatar da ƙudiri kan karfin ikon kaddamar da yaki, don taƙaita ƙara kai hare-hare Venezuela, inda ake shirin kaɗa ƙuri'a domin gabatar da ƙudirin a matakin ƙarshe, 'yan kwanaki bayan jami'an Amurka sun ɗauke Shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa Cilia Flores da ƙarfin tuwo, a wani abin mamaki a ranar 3 ga Janairu, inda aka hallaka mutane aƙalla 100 a farmakin.
A wani abin mamaki, 'yan Republican biyar sun shiga cikin dukkan Sanatoci 'yan Democrat na Majalisar Dattawa a ranar Alhamis inda suka kada kuri'a da nufin takaita ikon Shugaba Donald Trump dangane da rikicin da ke ƙaruwa da Caracas.
An amince da ƙudirin neman rage ƙarfin ikon yaƙi inda sanatoci 52, suk goyi baya 47 kuma suka ƙi amincewa da ita.
Kudurin yanzu zai tafi Majalisar Wakilai, inda babu tabbas kan makomarsa, la'akari da ƙin amincewa da aka yi a baya da kuma yiwuwar hawa kujerar na ƙi daga Trump, duk da ƙaramin rinjayen da Republican ta samu.
Trump ya ce Amurka za ta kula da Venezuela
Wannan na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin cewa Amurka za ta iya kula da Venezuela kuma ta sarrafa kuɗaɗen man fetur dinta cikin shekaru masu zuwa.
A yayin wata hira da New York Times ta bayyana a matsayin hirar awa biyu da aka tattauna batutuwa da dama, jaridar ta ce alamu na nuna cewa Trump ya dakatar da barazanar ɗaukar matakin soja kan makwabciyar Venezuela, Colombia.
Trump ya gayyaci shugaban 'yan gurguzua na Colombia, wanda ya taba kiran sa da ”mara lafiya”, ya ziyarci Washington.
"Lokaci ne kawai zai nuna" tsawon lokacin da Amurka za ta kula da Venezuela, in ji Trump. Lokacin da jaridar ta tambaye shi ko zai kasance watanni uku, watanni shida, shekara ko fiye, Trump yace:
"Zan iya cewa za a ɗauki lokaci fiye da haka."
Tsarin Mulkin Amurka yana buƙatar kowanne shugaban ƙasa ya sami amincewar Majalisar Dokoki kafin ya ƙaddamar da aikin soja na dogon lokaci.
Sanatocin da ke adawa da kudurin iko na yaki sun ce kama Maduro aiki ne na 'yan sanda, ba aikin soja ba.
Maduro yana fuskantar shari'a a kotun Amurka kan zarge-zargen miyagun ƙwayoyi da makamai, inda ya musanta laifin.















