TURKIYYA
3 minti karatu
Wasan kwaikwayon ‘Teskilat’ na Turkiyya ya yi duba kan kisan fararen hula a yaƙin Gaza
Fitaccen wasan kwaikwayon Teskilat ya nuna yadda ake cutar da fararen hula a yaƙin Gaza, da yadda ake jefa bama-bamai kan asibitoci da amfani da yunwa a matsayin makami a cikin sabon zango na fim din.
Wasan kwaikwayon ‘Teskilat’ na Turkiyya ya yi duba kan kisan fararen hula a yaƙin Gaza
Wasan kwaikwayon ‘Teskilat’ na Turkiyya ya yi duba kan kisan fararen hula a yakin Gaza / TRT
2 awanni baya

Shahararren wasan kwaikwayo na TRT Teskilat ya sanya tasirin jinƙai na rikicin Gaza a cikin sabon zangonsa, ta hanyar amfani da tattaunawa mai kaifi don fayyace cutar da fararen hula da aka yi.

A cikin wata fitowa ta baya-bayan nan, manyan jarumai sun tattauna mummunan tasirin ayyukan soja, suna yin magana game da "asibitoci da sansanonin da aka jefa bama-bamai" da kuma kwatanta "yunwa" a matsayin "sabon makami."

Tattaunawar har ma ta haɗa da amfani da kalmar "kisan ƙare dangi" a cikin musayar kalamai a wasan kwaikwayon game da Gaza.

Wani daga cikin ‘yan fim din ya yi kashedin, "Ayyukanmu sun zama masu ban tsoro," yana nuni da asarar fararen hula da halaka, yayin da wani ya amsa, "Muna cikin yaki kuma ba za mu iya yin kasa a gwiwa ba," yana jaddada tashin hankali tsakanin manufofin soja da damuwa ta bil'adama.

‘Wanda aka taba zalinta ta kisan ƙare dango, a yanzu yana kisan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a Gaza’

Wani ɗan fim din ya sake yin nuni kan maangar kasashen duniya, inda ya nuna cewa ƙasarsu, “waccae a baya aka taɓa zalinta ta hanyar kisan ƙre dangi, a yanzu duniya na kallonta a matsayin mai kashe waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a Gaza,” inda wani ya sake nanata cewa “waɗancan yankunan namu ne” yana mai kira da a sake jajircewa.

Masu shirya fim ɗin sun fitar da wani gajeren bidiyo na wajen, wanda ke nuna yadda ake kwaikwayon tambayoyin da suka shafi kare fararen hula da dokokin yaƙi.

Ta hanyar sanya wannan tattaunawa a waje mafi muhimmanci a fim din, wasan kwaikwayon Teskilat na nuna tattaunawar da ake ci gaba da yi a tsakanin jami’an diflomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula da tavvatar da cewa kafafen yada labarai sun yi adalci, da ba da damar shigar da agaji da ma ƙalubalen yaƙi a zamanance.

Wasan kwaikwayon da ke fayyace gaskiyar abin da ke faruwa

Israel continues to kill civilians in Gaza—more than half of them children—while the West moves toward recognising Palestine and international voices condemn the use of hunger as a weapon.

A cikin watan Agusta, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Gaza a matsayin mummunan yanayi na yunwa da ta taba samun kanta a ciki. Hukumomin ba da agaji na kasa da kasa sun yi gargadi game da bala'in yunwa a fadin yankin.

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton aƙalla mace-mace 440 daga yunwa da rashin abinci mai gina jiki, kuma kusan rabin wannan alƙaluma yara ne.

Fiye da Falasdinawa 2,000 ne aka kashe a yunkurin zuwa wajen manyan motocin agaji ko jira a wuraren rarraba kayayyakin agaji.

Tun a ranar 7 ga Oktoba, shekaru biyu da suka gabata, hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa 65,344 tare da jikkata wasu dubbai.