Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce jawabin da zai gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya zai mayar da hankali ne kan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, inda ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don kare Falasɗinawa da kuma ciyar da yarjejeniyar ƙasashen biyu gaba.
Da yake jawabi a filin jirgin saman Ataturk na Istanbul kafin ya tashi zuwa birnin New York a ranar Lahadi, Shugaba Erdogan ya ce, "A cikin jawabina a Majalisar Dinkin Duniya, zan yi tsokaci kan yanayin da ake ciki a Gaza, da kuma ƙoƙarin Turkiyya na kare zaman lafiya a yankin."
Ya ce taron UNGA na bana zai sha bamban da na baya, saboda "ƙasashe da dama za su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa".
Bayan ya isa cibiyar Turkevi da ke New York, Erdogan ya shaida wa manema labarai cewa ganawar da zai yi da shugaban Syria Ahmed al Sharaa a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, da kuma shugaban Amurka Donald Trump a Washington, na da matuƙar muhimmanci saboda "sun shafi batun yankin."
"A gare mu, kowane mataki da aka ɗauka a Gabas ta Tsakiya yana da matuƙar muhimmanci, kuma ba shakka, muna buƙatar mu tattauna waɗannan batutuwa da Shugaba Trump," in ji shi.
Shugaban ya bayyana fatansa na cewa, ci gaba da amincewa da Falasɗinu, zai sa a ‘‘gaggauta aiwatar da shawarwarin samar da ƙasashen biyu,’’ ya kuma ƙara da cewa batun hakki da tsaron 'yan Turkiyya da ke Cyprus ma zai kasance cikin ajandarsa.
Erdogan ya ce zai gana da Trump a yayin taron domin tattaunawa kan batun haɗin gwiwa kan kasuwanci da masana'antar tsaro, yayin da ya jaddada cewa "tsarin MDD a halin yanzu bai isa ya sauke nauyin da ke kansa ba".
‘‘A yayin ganawar tamu, za mu tattauna batutuwan da za su karfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, tare da mai da hankali kan harkokin cinikaiya, zuba jari, da kuma masana'antun tsaro.
Batutuwan da suka shafi yankunanmu za su kasance a kan gaba a ajandarmu, "in ji Erdogan yana mai nuni kan ganawarsa da Trump da ke tafe.
Shugaban na Turkiyya ya kuma ce zai gana da al Sharaa da ministan harkokin wajen ƙasar Asaad Al Shaibani a birnin New York na Amurka, wanda shi ne karon farko cikin shekaru da dama da aka samu wakilcin shugabancin ƙasar Syria a zauren MDD.
“'Yan'uwanmu maza da mata a Siriya sun biya maƙuɗan kuɗaɗe don samun 'yancinsu. Muna fatan Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ba da gudunmawa ga 'yancin Syria,” in ji Erdogan yana mai ƙari da cewa Turkiyya na son "zama zaman lafiya a kowane wuri na yankinmu."
A birnin New York, Erdogan zai kuma gana da 'yan ƙasar Turkiyya mazauna Amurka, kazalika zai yi gana da masana da manyan ‘yan kasuwan Amurka daban-daban.