‘Yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya sun kai hari a sansanin soja da daddare, lamarin da ya tilasta wa kimanin fararen hula 5,000 tserewa zuwa Kamaru, in ji majiyoyin tsaro da shaidu a ranar Juma’a.
A bana an sake fuskantar ƙaruwar tashin hankalin daga ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram da kuma reshenta na ISWAP suka haddasa, inda duka biyun suka shafe lokaci mai tsawo suna tayar da ƙayar baya a ƙasar da ke yammacin Afirka.
Harin daren da aka kai garuruwan Banki da Freetown, wanda ke kusa da iyakar Kamaru, ya faru ƙasa da mako biyu bayan wani hari da aka kai wa mutanen da aka sake tsugunarwa sakamakon rikici a Darul Jamal, inda aka kashe kusan mutane 90.
Shaidu sun ce ƙungiyar Boko Haram ce ta kai harin, inda mayaƙanta suka afka Banki kusan ƙarfe goma sha biyu na dare, kuma wani farar hula ya rasa ransa a musayar wuta tsakanin sojoji da maharan.
“Sojoji sun yi bajinta sosai”
“Ko’ina mutane suna ihu suna gudu,” in ji wata mazauniyar Banki mai suna Amina Bakari, wadda ta tsere ta haye iyaka zuwa Kamaru.
Ayuba Isa, wanda soja ne kuma mataimakin kwamandan sansanin sojoji na Banki, ya ce ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kwace sansanin kafin ƙarin sojoji su iso suka fatattake su.
“Mutanenmu sun yi bajinta sosai har muka iya korar su,” in ji shi. “Abin takaici, fararen hula sun riga sun tsere kuma gidaje da yawa sun lalace.”
Rahoton sa ido na tsaro da aka shirya wa Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda AFP ta gani, ya tabbatar da cewa maharan na cikin ISWAP ne.
Ya ce an kira rundunar sojojin sama domin taimako, aka dakile harin, amma sojoji biyu da fararen hula biyu sun mutu, sannan mutane 5,000 suka tsere zuwa Kamaru.
Tun daga shekarar 2009, rikicin ya kashe fiye da fararen hula 40,000 kuma ya tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.