Gwamnonin Nijeriya da Shugaban Ƙasa ya taɓa dakatarwa sannan ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihohinsu
NIJERIYA
4 minti karatu
Gwamnonin Nijeriya da Shugaban Ƙasa ya taɓa dakatarwa sannan ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihohinsuGwamnan farko da aka fara dakatarwa a irin wannan lamarin shi ne Joshua Dariye, wanda tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya dakatar bayan fama da tashe-tashen hankula na addini da ƙabilanci, musamman a garuruwan Yelwa–Shendam da kewaye.
Joshua Dariye na Filato da Ayodele Fayose na Ekiti da Siminalayi Fubara da Ribas ne aka taɓa dakatarwa sannan aka saka dokar ta-ɓaci a jihohinsu / Others
18 Satumba 2025

Kantoman Jihar Ribas Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya a ranar Laraba ya miƙa mulki ga Gwamna Siminalayi Fubara bayan shafe wata shida ana cikin dokar ta-ɓaci wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka a jihar.

Saka dokar ta-ɓacin ta biyo rikicin siyasa da na tsaro da ya tsananta a jihar ta Ribas.

Rikicin ya samo asali ne daga rikici mai tsawo tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, wanda ya ƙara muni bayan rushewar ginin majalisar a shekarar 2023.

Dangane da wannan tirka-tirkar siyasar, bari mu yi nazari dangane da wasu lokuta da aka taɓa saka irin wannan dokar ta-ɓacin a Nijeriya.

 Joshua Dariye

A wancan lokacin, Jihar Filato tana fama da tashe-tashen hankula na addini da ƙabilanci, musamman a garuruwan Yelwa–Shendam da kewaye, inda rikici tsakanin al’umma ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane da ƙona ƙauyuka, da kuma tarwatsewar dubban jama’a.

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya saka dokar ta-ɓaci a shekarar Mayun 2004 a Jihar Filato.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a lokacin ta zargi Joshua Dariye da cewa ya gaza shawo kan rikicin kuma yana nuna son kai wajen gudanar da lamarin.

Saboda haka, Shugaba Obasanjo ya sanar da dokar ta-ɓaci, inda ya dakatar da Dariye daga mukaminsa, sannan ya nada Janar Chris Alli (mai ritaya) a matsayin Kantoma na Jihar Filato na tsawon watanni shida.

A lokacin wannan mulkin na wucin-gadi, kantoman ya karɓe iko daga zaɓaɓɓiyar gwamnatin jihar sannan aka rusa majalisar dokoki ta jihar, sannan aka yi ƙoƙarin dawo da zaman lafiya kafin daga baya a mayar da iko hannun Joshua Dariye bayan an kammala wa’adin dakatarwar.

Ayodele Fayose

An bayyana dokar ta baci a Jihar Ekiti a ranar 19 ga Oktoba, 2006, a lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo.

A Oktoban 2006 ne gwamnatin Olusegun Obasanjo ta sanar da dokar ta-ɓaci a a Jihar Ekiti.

An tuhumi Gwamna Ayodele Fayose da rashin ɗa’a da cin hanci da cin da amfani da ofishin gwamnati domin biyan buƙatar kai.

Bugu da ƙari, jihar ta fada cikin rikicin siyasa da rikice-rikicen tashin hankali, ciki har da zargin cewa Fayose na da hannu a kisan kai saboda siyasa.

Sakamakon wannan rashin kwanciyar hankali, majalisar dokokin jihar Ekiti ta yi ƙoƙarin tsige shi, sai dai wannan yunƙurin ya haddasa rikici inda al’amura suka dagule har aka kusan gagara gudanar da gwamnati a jihar.

Domin mayar da martani kan wannan lamarin, sai gwamnatin Shugaba Obasanjo ta saka dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da majalisar jihar da dakatar da Fayose, inda ya saka Janar Adetunji Olurin mai ritaya a matsayin kantoma a jihar har sai da komai ya lafa.

Siminalayi Fubara

A watan Maris ɗin 2025, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa da na tsaro da ya tsananta a can.

Rikicin ya samo asali ne daga rikici mai tsawo tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, wanda ya ƙara muni bayan rusa ginin majalisar a shekarar 2023.

‘Yan majalisar sun yi ƙoƙarin tsige gwamnan, abin da ya sa gwamnati ta tsaya cik saboda kasa amincewa da kasafin kuɗi.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Rivers ta gaza gudanar da mulki da tsaron jama’a, abin da ya ba shi damar amfani da ƙarfinsa da doka ta ba shi a ƙarƙashin sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 don shiga tsakani.

Wannan ne ya sa ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida, sannan ya naɗa kantoma na musamman, mai ritaya, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin mai kula da jihar.

Bayan watanni shida da gwamnatin tarayya ta jagoranci jihar, a ranar 17 ga Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓacin tare da dawo da gwamnan, mataimakiyarsa da kuma ‘yan majalisar, wanda hakan ya kawo ƙarshen wannan matakin na musamman.