Gwamnatin Saudiyya ta sako wasu ‘yan Nijeriya uku da aka tsare bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a lokacin da suka je Aikin Umara a cikin watan Agusta.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ce ta sanar da hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba.
Daraktan yada labarai da yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa sakin nasu ya biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin hukumar ta NDLEA da gwamnatin Saudiyya.
Ya ce nan ba da jimawa ba maniyyatan za su koma Nijeriya.
“Hukumomin Saudiyya sun saki wasu mahajjata ‘yan Nijeriya uku da aka tsare a Jeddah tun watan da ya gabata bayan kama su bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
“Yan Nijeriya uku da aka saka bayan tsare su tsawon makonni hudu sun hada da Maryam Hussain Abdullahi da Bahijja Abdullahi Aminu, da Abdulhamid Saddieq,” in ji mai magana da yawun hukumar.
Kazalika, Babafemi ya shawarci matafiya a jiragen sama da a ko yaushe su tabatar sun yi wa kayansu alama mai kyau kafin su tashi don guje wa sharrin masu safarar ƙwaya.
A ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata ne hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta ce ta kama tare da tsare wani “ƙasurgurmin mai safarar ƙwaya” da wasu mutum biyar bisa zarginsu da kitsa da tura miyagun ƙwayoyi ta hanyar yi wa wasu ‘yan Nijeriya uku da suka tafi Aikin Umara “sharrin” cewa kayansu ne.
Makon ɗaya kafin nan ne hukumomin Saudiyya suka kama mutum ukun a birnin Jeddah bayan gano miyagun ƙwayoyi a cikin kayansu.
NDLEA a lokacin ta ce ta ƙaddamar da bincike ne bayan da ‘yan’uwan alhazan suka shigar da ƙorafi ga shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa, kuma sakamakon ne ya sa aka gano masu hannu a lamarin, wadanda suke gudanar da ayyukansu a filin jirgin saman Malam Aminu da ke Kano.
Yadda abin ya faru
Hukumar NDLEA ta ce abin ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan Nijeriya uku Maryam Hussain Abdullahi da Bahijja Abdullahi Aminu da Abdulhamid Saddiq suka hau jirgin Ethiopian Airline daga Kano zuwa Jeddah a ranar 6 ga Agustan nan, inda cikin rashin sa’a aka saka wa wasu jakunkuna shida da ba nasu ba sunayensu, kuma uku daga cikin maƙare suke da miyagun ƙwayoyi.
“Maryam Hussain Abdullahi ta hau jirgin da jaka ɗaya ne kawai mai nauyin kilo 9, sai dai bisa rashin sa’a ba ta sauka da kayan nata ba. Sai ana saura kwana ɗaya su bar Saudiyya, wato ranar 16 ga wata sannan aka sanar wa mijin Maryam cewa an ga kayansu.
“Bayan wannan zargin ne sai aka tsare ta a Jeddah inda har yanzu take can a tsare.”
NDLEA ta ce binciken da ta ƙaddamar ne ya sa ta gano cewa “an shigar da jakankuna masu ɗauke da ƙwayar ne da sunayen waɗancan mutanen na farko, kuma wasu gungun masu aikata miyagun laifuka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano ne suka yi hakan ba tare da sanin mutanen ba.
“Daga baya bincike ya gano duka jakankunan na wanin Ali Abubakar ne, wanda aka fi sani da Bello Karama, wanda shi ne jagoran gungun da suka shigar da jakankunan cikin jirgin Ethiopia a ranar 6 ga Agustan, wato ranar da alhazan nan suka tafi Umara.
“Sai dai wani abin mamaki shi ne shi Ali Abubakar din wanda shi ma Umarar zai tafi, jirgin saman Egypt Airlines ya bi maimakon na Ethiopia da aka loda jakankunansa masu ɗauke da ƙwayoyin a ciki.”
NDLEA ta ce bincikenta ya gano cewa wasu ma’aikatan kamfanin jigilar kaya a filin jirgin sama na Skyway ne suka saka sunan waɗancan mutanen cikin sirri ba tare da saninsu ba a kan jakankunan tare da loda su a cikin jirgin.
“Jakankunan da aka saka wa sunayen waɗancan mutanen su ne aka kama a Saudiyyan aka kuma gano cewa miyagun ƙwayoyi ne a ciki.”
Hukumar ta ci gaba da cewa a bisa waɗannan dalilan ne aka kama waɗannan mutanen ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Bisa bayanan da NDLEA ta tattaro zuwa yanzu ta gano cewa an riƙe Maryam Abdullahi ne da sauran mutum biyun bisa tuggun da wannan gungun masu aikata kaifin na filin jirgin saman Aminu Kano suka ƙulla.
NDLEA ta ce tuni ana tsare da mutum shida daga cikin gungun, kuma har an shigar da ƙarar huɗu daga cikinsu kotu.
Sannan a binciken farko da hukumar ta gudanar, mutum biyu a cikinsu sun tabbatar da cewa su suka kitsa lamarin bayan karɓar ladan aikin naira 100,000 daga Ali Abubakar, mai ainihin kayan.