Ma’aikata 10 na Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya da na kamfanin United Capital Plc, UCP sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a Gogon Ginin Afriland Towers da Titin Broad, na birnin Legas.
Sanarwa daban-daban da FIRS da UCP suka fitar sun tabbatar da mutuwar ma’aikatan.
A yayin da FIRS suka ce sun rasa m’aikata hudu, UCP kuma sun bayyana rasa nasu ma’aikatan shida sakamakon ibtila’in.
Wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban FIRS, Dare Adekanmbi, ya fitar ta bayyana sunayen wadanda ibtila’in ya shafa da Misis Ekelikhostse George (Mataimakiyar Darakta), Mista David Sunday-Jatto (Mataimakin Darakta), Misis Nkem Onyemelukwe (Babban Manaja), da Mista Peter Ifaranmaye (Manaja).
Wadanda suka mutu din na aiki ne a hawa na shida da na bakwai na ginin da ke dauke da ofisoshin FIRS guda biyu, a lokacin da lamarin ya faru.
Sanarwar ta kara da cewa "Cikin jimami da bakin ciki FIRS na sanar da mummunar asarar ma'aikatanta hudu sakamakon gobarar da ta tashi a Afriland Towers."
Hukumar ta ce ofis dinta na Tantance Matsakaicin Haraji da na Harajin Onikan na a ginin da gobarar ta kama.
Sanarwar ta kara da cewa jami’anta na tabbatar da Tsaro sun yin sauri wajen tuntubar ‘yan kwana-kwana, amma bakin hayaki ya riga ya turnuke ginin.
Hukumar ta FIRS ta kuma ce manya da kananan ma’aikatanta na cikin matukar kaduwa kuma sun isa ga iyalan wadanda suka mutu, tare da yin alkawarin bayar da duk wani tallafi da ya dace.
"Muna aiki tare da hadin gwiwar dukkanin hukumomin da abin ya shafa a Legas don gano musabbabin faruwar lamarin, yayin da ake ci gaba da yin hakan, za mu sake duba matakan kariya a ofisoshin FIRS da ke gine-ginen haya da mallakinta a fadin kasar," in ji sanarwar.
Kamfanin UCP ma ya bayyana alhinin rashin ma'aikatansa, inda ya bayyana wadanda gobarar ta shafa a matsayin "babban bangare" na "kamfaninmu da danginmu".
Sanarwar ta kara da cewa "Asara mai raɗaɗi ta bar wani gibi marar misaltuwa."
Firgici ya mamaye Titin Broad a ranar Talata lokacin da hayaki daga ginin ya tilasta kwashe mutane.
Bidiyon da aka dauka a wajen ya nuna yadda mazauna ofis din ke tsalle suna fadowa saboda tsoro, inda masu kallo ke kai agaji da tsani da katifu don taimaka musu.
Ma’aikatan da ibtila’in ya rutsa da su sun dinga farfasa tagogin gilashi don yin numfashi, yayin da mazauna kasa suka bude hannayensu don tarar su.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta ce gobarar ta samo asali ne daga dakin na’urar inverter da ke hawa na farko na dogon ginin Afriland Tower.
Shaidun gani da ido sun bayyana ganin mummunan lokaci, tare da yin kururuwa a fadin Titin Broad yayin da hayaki ya bazu cikin sauri a hawa na saman ginin.
Hotunan da aka dauka sun kuma nuna hayaki ya turnuke a benayen ginin, inda dole aka bude tagogi don samun iska.
Mutanen da ke ginin da dama sun yi cirko-cirko a bakin tagogi, suna tsere wa hayaƙi mai yawa wanda ke yaɗuwa cikin sauri a ginin.
Daga baya hukumar kashe gobara ta tabbatar da faruwar ibtila’in gobarar, ko da yake tuni hayaki ya mamaye hawa da dama na ginin.