Gwamnatin jihar Sokoto ta dakatar da wasu shugabannin makarantu shida bisa zargin rashin bin doka da kuma karbar kudade ba tare da izini ba dangane da sakamakon jarabawar karamar sakandare (JSS).
Kwamishian Ilimi a matakin farko da na sakandare na jihar, Ahmad Ila ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Ibrahim Iya ya fitar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
“Ba a yarda wani shugaban makaranta ya yi wani abu da ya saɓa wa doka ko tatsar ɗalibai da iyayensu ba,” in ji Kwamishina Ila.
Ya kara da cewa "Dole ne a tafiyar da makarantunmu ta hanyar da ta dace, ba da son rai ba."
Kwamishinan ya kuma ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani jami’in da aka samu da laifi.
Shugabannin da abin ya shafa sun fito ne daga Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Nana, da Makarantar Sakandare ta Gwamnati (GDSS) Gagi da GDSS Mana da Giginya Memorial College da Mana Basic Secondary School da kuma GDSS Silame.
A cewar sanarwar, an saka wa shugaban GDSS Silame takunkumi musamman saboda rashin biyayya.
Domin magance zarge-zargen, kwamishinan ya kafa kwamitin bincike mai mutane biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Tukur.
Sauran mambobin sun hada da Babban Sakataren AIEB, Daraktan Tabbatar da inganci a MOBSE, Daraktan Tsare-tsare a Hukumar Kula da Ayyukan Malamai, da Daraktan Tabbatar da Inganci a AIEB, wanda kuma zai zama sakataren kwamitin.
An umurci shugabannin makarantun da aka dakatar da su miƙa dukkan ayyukan gudanarwa ga mataimakan shugabanninsu da ke kula da harkokin gudanarwa nan take.
Har ila yau, ma’aikatar ta jaddada kudirinta na tabbatar da ɗa’a, gaskiya da riƙon amana a fadin makarantun gwamnati a jihar.