| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Sojojin Nijeriya sun kashe Aminu Kanawa, mataimakin Bello Turji
Haka kuma sojojin Nijeriyar sun kashe wasu muhimman kwamandojin Bello Turji waɗanda suka haɗa da Abu Dan Shehu da Jabbi Dogo da Dan Kane da Basiru Yellow da Kabiru Gebe da Bello Buba da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe.
Sojojin Nijeriya sun kashe Aminu Kanawa, mataimakin Bello Turji
Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kashe Aminu a wani samame da suka kai tsakanin 20 zuwa 21 ga Janairun 2025. / Hoto: Operation Fansan Yamma / Others
22 Janairu 2025

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga, Aminu Kanawa wanda shi ne mataimakin Bello Turji.

Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kashe Aminu a wani samame da suka kai tsakanin 20 zuwa 21 ga Janairun 2025.

Kashe Aminu Kanawa na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan sojojin na Operation Fansan Yamma sun kashe ɗan Bello Turji a wani samame da sojojin suka kai a Fakai.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ta Operation Fansan Yamma Laftanal Kanal Abubukar Abdullahi ya fitar, baya ga kashe Kanawa, sojojin sun kuma jikkata wasu daga cikin shaƙiƙan Bello Turji waɗanda suka haɗa da Dosso wanda ƙaninsa ne da kuma Danbokolo wanda makusanci ne ga Bello Turji.

Haka kuma sojojin sun kashe wasu daga cikin kwamandojin Bello Turji waɗanda suka haɗa da Abu Dan Shehu da Jabbi Dogo da Dan Kane da Basiru Yellow da Kabiru Gebe da Bello Buba da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe.

Haka kuma sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’adda 24 da ke cikin sansanin Bello Turji da ke kusa da Gebe da ƙananan hukumomin Isa, da kuma Gidan Rijiya da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Harin RSF na watan Oktoban 2025 a Al-Fasher na Sudan ya kashe aƙalla mutum 6,000: Rahoton MDD
AU: Shugabannin Afirka sun ƙaddamar da taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da batun ruwa da sauyin yanayi
Afirka ce kan-gaba wajen faɗaɗa samar da lantarki ta hasken rana a shekarar 2025: Rahoto
Gwamnatin Ghana ta ba da umarnin sarrafa kashi 50 cikin 100 na koko a cikin ƙasar
Sudan: Aƙalla mutum 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kogin Nilu
Kasashe shida sun shiga Kwamitin Tsaro na Tarayyar Afirka
RSF ta kashe ƙananan yara a harin da ta kai wani masallaci a yankin Kordofan na Sudan
Saudiyya ta yi tur da RSF kan munanan ayyukanta a Al Fasher, ta buƙaci a ba da hanyar kai agaji
Mutum biyar sun mutu a hatsarin helikwaftan ɗaukar marasa lafiya a Libya
Yadda 'yan Somaliya suka gina wa tsohon shugaba ƙasarsu Farmaajo sabon gida
Sake dawo da ainihin martabar Afirka
RSF ta Sudan ta kai hari da jirgi maras matuƙi, ta kashe gomman mutane da yara
Dubban ‘yan kasar Libya sun taru don halartar jana'izar Saif al-Islam Gaddafi
Harin RSF a wani asibiti a Sudan ya kashe mutum 22, ciki har da ma'aikatan jinya
Ghana da Zambia sun ƙulla yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba yayin ziyarar Mahama
Saif al-Islam Gaddafi: An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi
Afirka na fuskantar tarnaƙin bashin dala biliyan 90 a 2026, in ji S&P
Yadda Biteye na Senegal ke amfani da ƙwallon ƙafa don samun waraka ga ƙwaƙwalwa
Sojojin Rasha sun taimaka wajen daƙile hari a filin jirgin saman Nijar: Moscow
'Yanbindiga sun kashe sojojin Libya uku a kusa da kan iyakar Nijar