| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Pakistan da Turkiyya sun yi alƙawarin zurfafa alaƙar tsaro a ziyarar manyan jami'ai zuwa Ankara
Ziyarar na zuwa ne yayin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin zurfafa dangantaka tsakaninsu.
Pakistan da Turkiyya sun yi alƙawarin zurfafa alaƙar tsaro a ziyarar manyan jami'ai zuwa Ankara
Tawagar Pakistan ta kuma ziyarci hukumomin 'yansanda da yaƙi da ta'addanci da shige da fice da yaƙi da safarar mugayen ƙwayoyi — Photo: X/@TallalPMLN / TRT World
23 Fabrairu 2026

Ƙaramin ministan tsaron cikin gida na ƙasar Pakistan Talal Chaudhry ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Ankara, yana mai jaddada jajircewar Islamabad ga ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi tare da Turkiyya a fannin tsaro da yaƙar ta’addanci da shawo kan safarar miyagun ƙwayoyi, in ji jami’ai.

Chaudhry ya jagoranci wata tawaga wadda ta ƙunshi sakataren tsaron cikin gida da shugabannin muhimman hukumomin tsaron cikin gida.

Yayin ziyarar, ɓangaren Pakistan ya gana da mataimakin ministan tsaron cikin gida na Turkiyya Munir Karaloglu da manyan jami’ai domin inganta haɗin kai tsakanin ma’aikatun tsaron cikin gida na ƙasashen biyu.

Tawagar ta kuma ziyarci hukumar ‘yansanda da hukumar yaƙi da ta’addanci da ta shige da fice da ta yaƙar safarar miyagun ƙayoyi domin cikakkiyar tattaunawa da zummar inganta haɗin kai da musayar shawarwari.

Game da azumin watan Ramadan, Chaudhry ya miƙa saƙon gaisuwa daga Firaministan Pakistani Shehbaz Sharif da kuma ministan tsaron cikin gida Mohsin Naqvi, yana mai jaddada jajircewar Pakistan na aiki tare daTurkiyya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma sakamako mai kyau.

Turkiyya ta shafe shekaru tana ƙaddamar da matakan yaƙar ta’addanci domin kashe wutar barazanar masu alaƙa da ta’addanci da ƙasar ke fuskanta, irin su barazanar da ke zuwa daga ƙungiyoyi irin su Daesh da PKK — wani ɓangare da Pakistan za ta iya fatan samun irin wannan ƙwarewar domin ita ma tana yaƙar ƙungiyoyin Daesh da Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP).

Ziyarar ta ƙaramin ministan Pakistan na zuwa ne yayin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin zurfafa dangantaka tsakaninsu .

A watan Yulin shekarar da ta gabata, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firaministan Pakistan Sharif sun jaddada jajircewarsu domin ƙarfafa haɗin kai a muhimman fannoni ciki har da kasuwanci da tsaro da makamashi da sadarwa da zuba jari.

A watan Satumbar shekarar 2025, ministan tsaron Turkiyya Yasar Guler ya ziyarci Islamabad domin halartar karo na 16 na taron cibiyar tattalin arzikin Turkiyya da Pakistan, inda ya bayyana girman alaƙa ta tattalin arziki da ke tsakaninsu.

Ya bayyana cewa ‘yan kwangilar Turkiyya sun kammala muhimman ayyuka 72 a faɗin ƙasar Pakistan waɗanda ƙimarsu ta kai dala biliyan 3.5, yayin da cinikayya tsakanin ƙasashen ta zarce dala biliyan 1.4 — ƙari na kashi 35 cikin 100 nan da shekara zuwa shekara — inda ɓangarorin biyu suke da niyyar cinikayyar su ta kai ga dala biliyan 5 .

Turkiyya ɗaya ce daga cikin ƙasashen da suka fi sayar wa Pakistan makamai, in ji SIPRI.