AFIRKA
3 minti karatu
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Mutanen da suka rasa matsugunansu sun bazu a wurare daban-daban a jihar Kordofan ta Arewa da kuma wasu garuruwa da dama a jihar White Nile, a cewar Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya.
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Fiye da mutane 62,000 ne suka rasa matsugunansu bayan da RSF ta kwace iko da Al Fasher a arewacin Darfur na Sudan. / AA
13 awanni baya

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya (IOM) ta sanar cewa mutum 1,205 ne suka rasa matsugunansu daga biranen Bara da Umm Ruwaba a Jihar Kordofan ta Arewa, yayin da wasu 360 suka rasa matsugunansu daga Al-Abbasiya da Delami a Kudancin Kordofan saboda taɓarɓarewar tsaro.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, IOM ta ce ƙungiyoyinta da ke aiki a ƙarƙashin shirin tantance adadin yawan ‘yan gudun hijira wato ‘Displacement Tracking Matrix program sun ƙiyasta cewa daga cikin waɗanda suka rasa matsugunansu daga Arewacin Kordofan, 580 sun tsere daga Bara, yayin da 625 suka bar Umm Ruwaba.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan gudun hijirar sun bazu a wurare daban-daban a Arewacin Kordofan da kuma wasu garuruwa da dama a jihar White Nile da ke kudancin Sudan.

Yawan adadin da aka samu na yanzu ya biyo bayan jerin hare-haren da aka kai a baya a Arewacin Kordofan, inda mutane 36,625 suka rasa matsugunansu tsakanin 26-31 ga watan Oktoba, a cewar hukumar.

A wata sanarwa ta daban, IOM ta ce mutane 360 ​​sun rasa matsugunansu a jihar Kordofan ta Kudu, ciki har da 180 daga Al-Abbasiya da 180 daga Delami, waɗanda suka koma wasu yankuna a jihar da kuma Tandalti a jihar White Nile.

A ranar Alhamis, hukumomin Sudan sun bayyana rahoton asarar rayukan da aka yi sakamakon harin jiragen sama marasa matuki da aka kai yankin Zareba al-Sheikh al-Burai a Arewacin Kordofan.

Masu AlakaTRT Afrika - Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista

Kisan kiyashi

A ɓangare guda, ƙungiyar likitoci ta Sudan ta ce dakarun RSF sun kashe fararen-hula 38 a garin Umm Dam Haj Ahmed a jihar.

Haka kuma a ranar Litinin, RSF ta sake kai hari a Umm Dam Haj Ahmed, inda ta take hakkin fararen-hula tare da raba kimanin mutum 1,850 da matsugunansu saboda rashin tsaro, a cewar hukumomin Sudan.

A ‘yan kwanakin baya bayan nan sai da rundunar RSF ta ƙwace iko da Bara bayan yaƙinta da sojojin Sudan, sai dai ta musanta kai hari kan fararen-hula.

A ranar 26 ga Oktoba, RSF ta ƙwace iko da birnin Al Fasher da ke jihar Darfur ta Arewa kuma ta aikata kisan kiyashi ga fararen-hula, a cewar ƙungiyoyin cikin gida da na ƙasashen waje, hakan ya biyo bayan gargaɗin cewa harin na iya raba ƙasar ta Sudan.

A ranar Laraba, shugaban rundunar RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da "Hemetti" ya amince da cewa dakarunsa sun "keta hakki" a Al Fasher, yana mai iƙirarin cewa an kafa kwamitocin bincike.

Tun daga ranar 15 ga Afrilun 2023, Sojojin Sudan da RSF suka soma yaƙi, wanda kawo yanzu yankin d ƙasashen duniya suka gaza yin sulhu.

Yaƙin ya kashe mutane 20,000 kuma ya raba sama da mutane miliyan 15 da matsugunansu, a cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da na cikin gida a Sudan.