Kungiyar Haɗin Kan Musulmi (OIC) za ta gudanar da wani taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashe mambobinta a ranar Alhamis domin tattauna mamayar Isra'ila na faɗaɗa matsuganan ‘yan-kama-wuri-zauna da kuma ƙoƙarin haɗa yankin da aka mamaye na Yammacin Kogin Jordan cikin ƙasar.
An shirya yin taron a Jeddah ne bisa bukatar Falasdinu "don daidaita matsayi da tattauna hanyoyin ɗaukar mataki don tunkarar waɗannan shawarwari marasa inganci" da matakan da ke nufin "canza matsayin doka, siyasa da na yawan jama'a na yankin Falasdinu da ƙoƙarin rushe mafarkin samar da tsarin kasashe biyu", in ji Sakatariyar Janar ta ƙungiyar a wata sanarwa.
A ranar 15 ga Fabrairu, gwamnatin Isra'ila ta amince da wata shawara ta yin rajistar manyan yankuna a cikin yankin da aka mamaye na Gabar Yammacin Kogin Jordan a matsayin "mallakin ƙasa" (state property), abin da ya faru a karon farko tun bayan mamayar da Isra'ila ta yi a 1967.
A cewar kafafen yada labarai na Isra'ila, matakin ya haɗa da buɗe hanyoyin rajistar ƙasa da aka dade ana dakatar da su, soke tsohuwar dokar Jordan da ta haramta sayar da ƙasa ga Yahudawa, da kuma bayyana bayanan rijistar ƙasa da aka boye tsawon shekaru aru-aru.
Falasdinawa na gargadin cewa matakan Isra'ila sharar fage ne na cikakkiyar mamaya da mallake Yammacin Kogin Jordan, wanda suke cewa zai kawo ƙarshen yiwuwar kafa ƙasar Falasdinu mai zaman kanta kamar yadda ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya ya tsara.
















