Me ya sa cutar cizon kare ke kashe dubban mutane a Afirka duk da cewa ana iya rigakafinta?
AFIRKA
5 minti karatu
Me ya sa cutar cizon kare ke kashe dubban mutane a Afirka duk da cewa ana iya rigakafinta?Cutar cizon kare na kashe mutum 59,000 a shekara, kashi 95 na mutuwar ke afkuwa a Afirka da Asiya, a yayin da karnukan da ba a yi wa allurar rigakafi ba ke kara yawa, rashin kayan magance cutar da rashin bayar da rahotanni na kara ta'azzara lamarin.
Cizon karnuka na iya saka wa mutum cutar cizon kare. Photo: GAVI
12 awanni baya

Kocin tsere na Kenya Dennis Mwanzo ya sunkuya don gyara wuraren fara tsere na yaransa a lokacin atisayen safe a ranar 3 ga Oktoba lokacin da ya ji wani abu ya kama ɗan sharabarsa ta dama.

Cikin tsoro, sai ya juya ya gano cewa wani kare da babu mai shi ya cije shi da yake tsaka da aikinsa.

Mwanzo ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka fuskanci harin kare a lokacin gasar Wasannin Nakasassu a filin wasa na Jawaharlal Nehru da ke New Delhi, India.

A wajen Mwanzo, wanda ke taimaka wa ɗan tseren mita 200 Stacey Obonyo ya shirya don bayar da horo, damuwar nan take ta wuce zafin da yake ji. Kamar duk wanda dabbar da ba a san ta ba ta cije shi, yana jin tsoron kamu wa da cutar cizon kare.

Mwanzo ya yi gaggawar zuwa Asibitin Safdarjung don neman magani kuma ya fitar da bidiyo daga baya don ya bayyana halin damuwar da ya shiga.

"Ina jin dama-dama yanzu. An yin min allurar rigakafi da dama, ciki har da maganin tetanus da cutar cizon kare," in ji shi.

Duk da cewa yankin Babban Birnin India na dauke da kusan karnuka miliyan ɗaya da ke yawo a tituna babu masu su, hatsarin cizon kare da ke yaɗa cutar cizon kare bai takaita ga ƙasa ɗaya kawai ba.

Afirka ma na da saurin kamuwa da cutar, inda yawan karnukan da suke yawo a tituna a sassa da dama na nahiyar ke haifar da ƙalubale ga lafiyar jama'a, jin daɗin dabbobi, da kuma kula da birane.

"Ambaton cutar cizon kare kawai abin tsoro ne," Dr. Traore Tiebe, jami'in kula da lafiyar dabbobi da cututtukan namun daji a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya fada wa TRT Afrika.

"Duk da cewa tana ɗaya daga cikin tsofaffin cututtuka da aka sani, har yanzu tana kashe mutane a wasu sassan Afirka, tana kashe dubban rayuka kowace shekara. Ana iya rigakfin waɗannan mace-macen."

Fahimtar me cece cutar cizon kare

Cizon kare wata cuta ce mai tsanani, mai yuwuwar kisa wadda kwayar cutar Rhabdoviridae ke haifarwa, kuma ana yada ta ga mutane ta hanyar hulɗa - musamman cizo da yakushi - tare da dabbobin gida ko na daji da suka kamu da cutar.

Kodayake ana samun cutar cizon kare a kowace nahiya, yawaitar ta a ƙasashen Afirka faskara. A birane da karkara, karnuka ne ke da alhakin yada cutar da kashi 99% na kamu wa da cutar a tsakanin mutane.

Masana sun ce yana da wuya a iya auna yawan kamu wa da cutar cizon kare a ƙasashen Afirka saboda ba a bayar da rahoton wasu mutane da yawa da ke kamu wa da cutar ba, musamman a yankunan karkara inda ake da ƙarancin damar zuwa wuraren kiwon lafiya da kayan aikin gwaji.

"Sau da yawa ba a bayar da rahoton kamu wa da cutar cizon kare, har amanana yin kuskuren gano cutar, shi ya sa ba mu da cikakkun bayanai," in ji Dr Traore.

Daduwar kamuwa da cutar a duniya

A duk duniya, cutar cizon kare na kashe kimanin mutane 59,000 kowace shekara, inda kusan kashi 95% na mace-macen ke faruwa a Afirka da Asiya.

Cutar tana shafar talakawa sosai, waɗanda galibi ba sa iya biyan kuɗi ko samun magani bayan fuskantar cizon (PEP), wato allurar rigakafi da za ta iya hana kamuwa da ita bayan cizo.

Yara suna cikin hatsari mafi girma. "Kusan kashi 40% na mutanen da dabbobin da ake zargi da kamuwa da cutar cizon kare suka cije su yara ne 'yan ƙasa da shekaru 15," in ji Dr. Traore. "Sha'awarsu ta halitta da kuma wasa da dabbobi na sanya su cikin hatsari mai girma."

Kwayar cutar cizon kare tana shiga jiki ta hanyar cizo ko karce wa kuma tana tafiya a hankali ta hanyar jijiyoyi zuwa kwakwalwa. Da zarar ta shiga kwakwalwa, tana haifar da kumburi wanda ke haifar da rudani, tsoron fitar ruwa, mutuwar barin jiki, da kuma mutuwa daga ƙarshe.

"Da zarar alamun kamu wa da cutar sun bayyana, kusan koyaushe tana kashe mutane," in ji Dr. Traore.

Nau'i biyu na cutar cizon kare na bayyana a cikin mutanen da suka kamu da cutar ta hanyar cizon kare. "cutar cizon kare mai zafi", wadda ta fi karfi, an san ta da haifar da fushi, firgici, da kuma tsoron fitar da ruwa a kwakwalwa.

"Cutar cizon kare masu janyo mutuwar barin jiki" na ci gaba a hankali, tana fara wa da raunin gabbai kafin ta sumar da mutum kuma daga nan kashe shi. Saboda yana kwaikwayon wasu alamomin cututtukan jijiyoyi, sau da yawa ana gano wannan nau'in cutar ta cizon kare ba daidai ba, wanda ke ba da gudunmawa ga rashin bayar da rahoton da ya kamata.

Rigakafi ya fi magani

Labari mai daɗi shi ne cewa ana iya rgakafin cutar cizon kare dari bisa dari ga dabbobi da mutane, tare da allurar rigakafi ga karnuka wanda wannan ce hanya mafi dacewa.

"Yin allurar rigakafi ga karnuka, gami da 'ya’yansu kanana, yana dakatar da kwayar cutar daga tushenta. Kashe karnukan da suke yawo a kan tituna ba mafita mai tasiri ba ce," in ji Dr Traore ga TRT Afrika.

Idan kare ya ciji wani, ko da dabbar ba mai yawo a titi ba ce tana da mai ita, kulawar gaggawa ga raunin ta hanyar yin allurar rigakafi na iya kawo bambanci tsakanin rayuwa da mutuwa.

"Wanke raunin sosai da sabulu da ruwa bayan fuskantar cizon dabbar da ake zargi da cutar cizon kare na da mahimmanci," in ji Dr Traore. Duk da haka, ya kamata a nemi taimakon likita cikin gaggawa.

Rumbun Labarai
China ta gargaɗi ‘yan kasarta su kauce wa hadarin zama bayin ma'adinai a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
Jam’iyyar FPO a Austria ta yi kira da a hana mata yin lullubi
Ghana za ta tura injiniyoyin soji don taimakawa wajen sake gina Jamaica bayan afkuwar guguwa
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Wata ƙungiya ta zargi kamfanin Nestle da sayar wa Afirka abincin jarirai mai sikari da yawa
Ranar Makewayi ta Duniya: Kundin tsafta na Afirka don inganta lafiya da mutunci
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa