Rundunar sojan Nijeriya ta ce wani kwamanda da wasu sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun rasa ransu a yayin wata arangama da mayaƙan Boko Haram a Jihar Borno a ranar Juma’a 17 ga watan Oktoba.
Wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojan Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Litinin ta ambaci sunan kwamandan a matsayin Laftanal Kanal Aliyu Paiko.
Sai dai ba ta ambaci yawan sojojin da aka kashe a arangamar ba, amma ta bayyana cewa kaɗan ne. A ɓangare ɗaya kuma ta ce an kashe ‘yan Boko Haram da dama, an kuma ji wa wasu masu yawa rauni.
Appolonia Anele ta ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, yayin da sojojin suka gano kuma suka lalata wani sansanin Boko Haram a lokacin da suke shirin kai wa jama’a hare-hare.
“Waɗannan jajirtattun gwararzan sun rasa ransu, saboda ƙasarmu, don haka za a ci gaba da tunawa da su har abada. Rundunar Sojan Nijeriya za ta ci gaba da martaba sadaukarwarsu, saboda rashinsu ya zo tare da ƙudirinmu na kawar da ta’addanci daga Nijeriya,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji wallafa hotunan jami’an da suka rasa ransu yayin fafatawar, har zuwa lokacin da za a sanar da iyalensu a hukumance, domin tausayawa da kuma mutuntawa a gare su.