NIJERIYA
2 minti karatu
Wajibi ne ɗalibai su ci Darasin Lissafi a jarrabawar kammala sakandare – Gwamnatin Nijeriya
A 'yan kwanakin nan ma'aikatar ilimi ta ƙasar ta ce za a daina tilasta wa ɗaliban da ke shirin karatun ɓangaren Arts cin darasin Lissafi, lamarin da ya jawo suka daga masana a ɓangaren ilimi waɗanda ke cewa hakan zai ƙara lalata ƙwazon ɗalibai.
Wajibi ne ɗalibai su ci Darasin Lissafi a jarrabawar kammala sakandare – Gwamnatin Nijeriya
Gwamnatin ta jaddada cewa sabon tsarin shigar ɗalibai jami’a bai sahale wa kowane ɗalibi ƙin zana jarrabawar lissafi ba. / Reuters
19 Oktoba 2025

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wajibi ne ga ɗaliban ƙasar da za su zana jarrabawar kammala sakandare su ci darasin Lissafi (Mathematics).

Mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folashade ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.

Tun a ranar Talatar da ta gabata, Boriowo ta sanar da cewa ɗaliban babban makarantar sakandare da ke karatun Arts ba za a sake tilasta musu su samu credit a darasin Lissafi ba a jarabawar SSCE don samun gurbin shiga jami’a.

Ta bayyana cewa an kawo wannan sauyi ne bayan shekaru da dama da aka yi ana taƙaita damar shiga jami’a ga ɗalibai da suka cancanta saboda rashin cin darasin Lissafi.

Ta ce duk da cewa fiye da ɗalibai miliyan biyu ke rubuta jarabawar UTME a kowace shekara, kusan 700,000 ne kawai ke samun gurbin karatu a jami’o’i.

Sai dai wannan matsaya ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu masana ilimi suka soki sauyin, suna cewa hakan zai ƙara lalata ƙwazon ɗalibai kuma ya rage ingancin su a fannin karatu.

Sai dai a cikin wani sabon bayani, Boriowo ta jaddada cewa sabon tsarin shigar ɗalibai jami’a bai sahale wa kowane ɗalibi ƙin zana jarrabawar lissafi ba.

“Dukkan ɗalibai dole ne su ci gaba da yin rajista da rubuta jarabawar Ingilishi da Lissafi a jarabawarsu ta O-Level,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ko da yake an ba jami’o’i dama su karɓi ɗalibai a wasu fannoni da ba sa buƙatar credit a Ingilishi ko Lissafi, amma har yanzu ɗalibai dole su rubuta waɗannan fannoni biyu a jarabawarsu ta O-Level.