Shin abin arziki ne bai karbi kare ba, ko kuwa dai an yi saka ne da mugun zare? Ina magana ne kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan afuwa da sassauta hukuncin da shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane 175 da kotuna suka yanke wa hukunci kan laifukan da suka aikata.
Abin da ya fi daukar hankali shi ne ganin sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka, cikin wadanda aka yafewa, musamman manyan masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi, da masu kisan kai, da masu garkuwa da mutane, da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da gaggan masu cin hanci da rashawa.
Cikin wadanda suka amfana da afuwa da ramgwamen hukuncin akwai Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa a 2020 saboda kisan mijinta wada ta kwashe shekaru shida a gidan yari; da Kelvin Oniarah Ezigbe, wanda ake yanke wa hukunci a 2023, saboda garkuwa da mutane hukuncin da ya fara aiki a 2013. Akwai kuma Manjo Janar Mamman Vatsa da aka zartar wa hukuncin kisa a 1986 saboda laifin shirya wa Janar Ibrahim Babangida juyin mulki.
Sannan daga cikin wadanda aka yi wa afuwar, akwai wadanda ma sun gama zaman gidan kaso, amma afuwar za ta iya ba su damar sake rikon wani mukami na gwamnati ko yin takara, kamar tsohon ɗan majalisar wakilan daga Jihar Kano, Farouk Lawan.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma madugun ‘yan hamayya na Nijeriya Atiku Abubakar cewa ya yi, babban abin damuwar shi ne, ganin yadda kashi 29.2 na wadanda aka yi wa afuwar, mutanen da aka yanke wa hukunci ne saboda laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.
Ita ma jam’iyyar hamayya ta ADC a ta bakin kakakinta, Malam Bolaji Abdullahi, cewa ta yi afuwar da aka yi wa mutanen abin takaici ne kuma kunyata kasa ne, sannan cin mutunci ne ga yunkurin Nijeriya na yaki da miyagun kwayoyi, da karfafa gwiwar aikata manyan laifuka, da kuma zubar wa da Nijeriya mutunci a idon duniya.
To sai dai a sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar dangane da yafiyar da Tinubu ya yi, Bayo Onanuga ya ce an yi wa mutanen afuwa ne saboda rahotannin cewa sun yi nadama, kuma sun kyautata halayyarsu, wasu kuma an yafe musu ne saboda tsufa da rashin lafiya, wasu kuma saboda sun koyi sana’o’i, wasu kuma saboda shiga jami’ar da ake karatu daga gida.
To amma bari mu yi karatun baya, inda za mu ga cewa ba a wannan karon ne irin wannan afuwar da shugaban kasa ke yi wa masu laifi take janyo ce-ce-ku-ce ba.
A shekarar 2022 Shugaba Buhari ya yafe wa fursunoni 159, cikinsu har da tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, da na Jihar Taraba, Jolly Nyame, wadanda aka daure saboda satar kudin jama’a, abin da ya janyo wa shugaba Buharin mummunar suka a lokacin.
A shekarar 2013, an yi wa Shugaba Goodluck Jonathan mummanar caccaka saboda yafe wa tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha, wanda aka daure saboda satar kudin jama’a, har ma kungiyar Transparency International ta ce ya kamata Jonathan ya soke afuwar da ya yi wa Alamieyeseigha.
Sashi na 175 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ne ya bai wa shugaban kasa da gwamnoni damar yafe wa mutanen da aka yankewa hukunci, ko kuma rage musu hukuncin da kotu ta yanke.
Asali, an fito da tsarin ne domin tausaya wa mutanen da aka daure, musamman inda aka samu an yi kuskure a shari’a, ko kuma hukuncin ya zarta girman laifin da aka yi.
Wasu masana dai na cewa, ya kamata Nijeriya ta yi koyi da Indiya wajen sanya wasu sharuda kafin a yi wa masu laifi afuwa.
Don haka suka ce ya kamata duk lokacin da za a yafe wa wasu fursunoni a ringa sara ana duban bakin gatari.