Majalisar Dokokin Nijeriya ta ba da shawarar a dawo da manyan zaɓukan ƙasar baya zuwa watan Nuwamban 2026 maimakon yin su a watan Fabrairun shekarar 2027.
An bayyana hakan ne a cikin Ƙudrin Dokar Zabe (da aka gyara) ta 2025, wadda aka gabatar yayin taron jin ra'ayin jama'a na hadin gwiwa na Kwamitocin Majalisar Dattijai da na Wakilai kan Harkokin Zaɓe da suka shirya a Abuja a ranar Litinin.
Idan har aka amince da wannan shawara, ke nan za a yi manyan zaɓukan Nijeriya wata shida kafin lokacin da aka saba yin su, wato a watan Fabrairu.
An yanke shawarar yin gyaran ne don tabbatar da cewa an kammala dukkan batutuwan da suka shafi zaɓe kafin ranar 29 ga Mayun 2027, wato lokacin miƙa mulki.
‘Yan majalisar, sun kuma bayar da shawarar ƙara ƙarfafa ɓangaren shari’a don warware matsalolin da suka shafi al’amuran zaɓe.
Sauran abubuwan da suka fi daukar hankali a cikin kudurin sun hada da bai wa fursunoni damar zaɓe, da bai wa ‘yan Nijeriya mazauna ƙsashen waje damar kaɗa ƙuri’a da wuri, da amfani da katin shaidar zama ɗan ƙasa, NIN wajen rajistar masu kaɗa ƙuri’a, da kuma miƙa sakamakon zaɓe ta intanet.
‘Yan majalisar sun ce matakin zai kawar da matsalar saye da sayar da ƙuri’a, waɗanda suka yawaita a zaɓukan da suka gabata, da kuma tabbatar da tantance masu kaɗa ƙuri’a gaba ɗaya.
Dokar Zabe (da aka gyara) ta 2025 ta ce dole ne majalisun biyu su amince da ita kafin a miƙa ta ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin ya amince da ita.