Aƙalla mutum 17 sun rasa rayukansu a wata mummunar arangama da ta faru tsakanin ’yan ta’adda da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a wani wurin da ake haƙar zinari a Jihar Kaduna, bisa wani rahoton tsaro na sirri da aka shirya wa Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Juma’a.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Birnin Gwari, wani yanki a arewa maso yammacin Nijeriya da ya daɗe yana fama da ta’addanci, satar shanu, da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa.
A cewar kafar watsa labarai ta TVC News ta Nijeriya, tashin hankalin ya fara ne a lokacin da wani gawurtaccen shugaban ɓarayin daji ya yi ƙoƙarin ƙwatar zinari daga hannun masu haƙar ma’adinai ta hanyar yi musu barazana da bindiga.
Sai dai masu haƙar ma’adinan sun ƙi yarda inda suka far masa har suka kashe shi. Wannan kisan ya tayar da hankali, inda ’yan tawagar shugaban da aka kashe suka dawo da makamai, suka kai farmaki suka kashe masu haƙar ma’adinai bakwai.
Washe gari rikicin ya bazu zuwa kauyen Layin Danauta da ke kusa. Maharan sun kashe mutane tara sannan suka jikkata mutum 13, sannan suka sace wasu mazauna garin, tare da lalata gidaje da dukiyoyi.
Yankin Birnin Gwari, wanda ke da albarkatun ƙasa da ƙasar noma, ya dan samu zaman lafiya bayan gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya hannu a yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindiga da al’ummomin yankin a Nuwamba 2024.
Sai dai wannan sabon tashin hankali ya tayar da hankalin jama’a, inda wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Kabir, ya bayyana damuwarsa kan wannan tashin hankali.
“Mun samu dan zaman lafiya tun bayan yarjejeniyar sulhu, amma wannan sabon tashin hankali yana iya kawo cikas ga zaman lafiyar,” in ji Kabir.
Abin da ke ƙara rikitar da lamarin yankin shi ne kasancewar ’yan ta’addar Ansaru, wata ƙungiya da ke da alaƙa da Al-Qaeda. Tun daga shekara ta 2021, rahotanni sun nuna cewa Ansaru ta kulla dangantaka da wasu kungiyoyin ’yan bindiga a yankin.
Ko da yake yawancin ’yan bindiga suna aiki ne saboda ribar kuɗi, ba saboda akida ba, masana tsaro sun gargaɗi cewa ƙarfafa alaƙa tsakanin su da kungiyoyin ta’addanci daga arewa maso gabas na iya ƙara tabarbarewar tsaro a yankin.