Turka-turkar kan batun yajin aiki tsakanin ASUU da gwamnatin Nijeriya
NIJERIYA
4 minti karatu
Turka-turkar kan batun yajin aiki tsakanin ASUU da gwamnatin NijeriyaƘungiyar ƙwadagon ta ce ba za ta miƙa wuya ba ga abin da ta kira ƙoƙarin gwamnati na raba kan malaman jami’o’i.
Ministan Ilimi na Nijeriya, Olatunji Alausa / Others
11 awanni baya

Ƙungiyar malam jami’a ta Nijeriya (ASUU) ta yi watsi da umarnin gwamnatin tarayya ta ‘babu albashi idan ba a je aiki ba’, tana mai jaddada cewa ƙungiyar ba za ta ji tsoron barzana ba.

Shugaban ƙungiyar ASUU, Chris Piwuna ne ya bayyana wannan ranar Litinin a a lokacin da yake bayani a gidal talabijin din Channels.

Ya ce kan ƙungiyar ya kasance a haɗe kuma ba za ta miƙa wuya ba ga abin da ya kira ƙoƙarin gwamnati na rarraba kawunan malaman makaranta.

“Ba ma mayar da martani ga barazana, kuma babu wanda ya isa ya yi mana barazana,” a cewar Piwuna.

Piwuna ya ce duk ƙungiyoyin malamai, irin su ƙungiyar malaman likitoci da likitocin haƙora (CONUA), suna a haɗe wajen goyon bayan yajin aikin.

“Yana mana barazana, yana rubuta wasiƙa zuwa NAMDA da CONUA, inda yake gaya musu cewa za su iya samun albashinsu. Yana son ya raba mu, amma kawunanmu a haɗe suke a kan wannan lamarin.

“CONUA na tare da mu, NAMDA na tare da mu, SSANU na tare da mu, NASU na tare da mu. Kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma Kwalejojin Ilimi ma suna tare da mu,” in ji shi.

Shugaban ya bai wa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, shawarar ya mayar da hankali kan warware jayayyar da ake yi maimakon yin baraza.

‘Babu albashi idan ba ka je aiki ba’

A ranar Litinin ne dai gwamnatin Tarayyara Nijeriya ta bai wa jami’o’i umarnin ƙaddamar da manufar ‘babu albashi idan ba ka je aiki ba’ kan malaman jami’a da ke cikin yajin aikin gargaɗi na mako biyu da ake yi.

Umarnin yana cikin wata wasiƙar da aka fitar ranar 13 ga watan Oktoba, wanda ministan ya sanya wa hannu.

Ministan ya bayyana rashin jin daɗin gwamnatin duk da tatatunawar da ake yi da kuma kiraye-kiraye na sansanci.

“Bisa ga tanade-tanaden dokoki da suka shafi ƙwadago, gwamnatin tarayya ta nanata matsayarta kan ɗabbaka manufa ta ‘babu albashi idan ba a je aiki ba’  kan ko wane ma’aikaci da ya gaza ayyukansa a hukumance a lokacin yajin aikin,” in ji wasiƙar.

Alausa ya kuma umarci shugabannin jami’o’i su yi ƙidayar malaman da ke makarantunsu su kuma miƙa rahotannin da ke nuna waɗanda suka zo aiki.

Ya ce malamai da ke cikin ƙungiyoyin CONUA da NAMDA, waɗanda ba sa cikin yajin aikin, an cire su daga cikin waɗanda umanin zai yi aiki a kansu.

Ministan ya ƙara da cewa shi ya bai wa hukumar NUC mai kula da jami’o’i umarnin sa ido kan biyayya ga manufar tare da ba da rahoto a kansa cikin kwanaki bakwai.

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa ta riga ta magance dukkan buƙatun ASUU kuma babu buƙatar yajin aikin.

Sai da kuma ASUU ta ce ba haka lamarin yake ba, tana mai cewa ba a cim ma wani muhimmin abu ba wajen magance matsalolin da ƙungiyar take ƙorafi a kansu.

Yajin aikin gargaɗi 

 

A ranar Lahadi, ASUU ta yi shelar wani cikakken yajin aiki na mako biyu na gargaɗi wanda zai shafi dukkan jami’o’in gwamnati a faɗin Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna ya ce matakin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 14 da ta bayar a ranar 28 ga watan Satumba na shekarar 2025.

“Babu wani mahimmin martani daga hukumomin da lamarin ya shafa, saboda haka an bai wa dukkan rassan ASUU umarnin su fara yajin aiki,” kamar yadda ya bayyana a wani taron manema labarai da aka yi a Jami’ar Abuja.

Ya bayyana cewa yajin aikin yana daidai da matsayar da aka cimma a taron kwamitin zartarwar ƙungiyar.

Piwuna ya ce yajin aikin ya zama dole saboda  jinkirin gwamnatin wajen amsa kiraye-kirayen ASUU da kuma watsi da yarjejeniyoyin da aka rattaɓa wa hannu a tun shekarar 2009.

“Yarjejeniyarmu ta shekarar 2009, wadda har yanzu ana sake tattauna ta bayan shekaru takwas, har yanzu ba a gama aiwatar da ita ba. Kiran da aka yi na janye yajin aikin ya zo a ƙurarren lokaci,” a cewarsa.