A wani muhimmin yunƙuri na daƙile safarar miyagun ƙwayoyi, rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Jigawa ta kama aƙalla mutum 105 da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a wani samame da ta kai sassa daban-daban na jihar a lokaci ɗaya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shi’isu Adam ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai ranar Talata a hedkwatar rundunar da ke Dutse, babban birnin jihar.
Adam ya bayyana cewa a jerin samamen da rundunar ta kai a baya bayan nan, jami’an rundunar sun shiga lunguna da saƙo na Jigawa domin kawar da harkar miyagun ƙwayoyi. “Jami’anmu sun yi iya ƙoƙarinsu,” a cewarsa, yana mai jaddada irin jajircewarsu wajen kawar da matsalar ƙwaya daga jihar.
Ya ce jerin samamen sun kai ga ƙwace miyagun ƙwayoyi da suka haura 5,000 ciki har da tabar wiwi da nau’o’in ƙwayoyi.
Kazalika, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ba da bayanai dalla-dalla na ƙwayoyi da aka ƙwace, lamarin da ya bayyana a matsayin mai girman gaske.
Cikin ababen da aka ƙwacen akwai ƙwayar Exol 2,541 da kuma ƙwayar D-5 1,146, waɗanda dukkansu ana shansu don maye.
Baya ga haka akwai fakitin Tramadol 270 da kuma fiye da ƙulli dubu ɗaya na tabar wiwi.
Sauran ababen da aka ƙwace sun haɗa da ƙwayar Diaxer 269 da kafso na Pregabalin 153 da kuma ƙwayar Farin Malam guda 82.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama sauran miyagun ƙwayoyi irin su Diazepam da Vegakris da kuma Calidon’s.
SP Adam ya bayyana cewa an ƙwace kuɗi da ya kai N92,460 tare da wasu kayayyaki kamar solisho da da madarar sukudai da giya mai ƙarfi.
“Wannan nasarar za ta aika saƙo mai ƙarfi ga waɗanda ke harkar ƙwayoyi,” in ji shi.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya yi kira ga al’umma su ci gaba da bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro ta hanyar ba da rahoto kan duk abin da ba su yarda da shi ba.