Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja babban birnin Nijeriya ta samu ‘yan ƙasashen waje 59 da laifi a cikin aika-aikar wata ƙungiya da ke tafka laifukan intanet wadda jami’an cibiyar laifukan intanet ta rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bankaɗo.
‘Yan ƙasashen ƙetaren da aka bayyana a matsayin ‘yan ƙasar China da ‘yan ƙasar Malaysia, suna cikin mutum 130 da aka kama a wani samame da ‘yan sanda suka kai wani gini a unguwar Jahi da ke birnin Abuja ranar 3 ga watan Nuwamba na shekarar 2024.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, CSP Benjamin Hundeyin, ya fitar ranar Alhamis ta ce waɗanda ake zargin da suka haɗa da ‘yan ƙasashen waje 113 da kuma ‘yan Nijeriya 17 an tuhume su ne da laifin zamba ta intanet da kutsen intanet da kuma wasu laifuka masu barazana ga tsaron intanet na ƙasar.
An yanke wa ashirin da ɗaya daga cikinsu hukunci a wata Agustan shekarar 2025, yayin da aka samu biyar daga cikinsu da laifi a watan Satumba.
Hundeyin ya ƙara da cewa hukuncin kotun na baya bayan nan ya mayar da adadin waɗanda aka samu da laifi a cikinsu mutum 85.
“A ci gaba da ƙoƙarin rundunar ‘yan sandan Nijeriya na daƙile dukkan nau’ukan laifukan intanet da kuma kiyaye tsaron ƙasa, rundunar ta hannun cibiyar daƙile laifukan intanet ta ƙasa, ta sake samun gagarumar nasara inda aka samu ƙarin ‘yan ƙasashen ƙetare 59 da laifi, a ci gaba da shari’ar mambobin wata babbar ƙungiyar laifuka ta intanet ta ƙasa da ƙasa da aka bankaɗo a Abuja a watan Nuwambar shekarar 2024,” in ji sanarwar.
“Ranar Asabar, 3 ga watan Nuwamba na shekarar 2024, yayin da suke aiki bisa bayanan sirri, jami’an cibiyar daƙile laifukan intanet na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, sun ƙaddamar da wani aiki na intanet a wani gini da ke unguwar Jahi, a Abuja.
“Aikin wanda wani ɓangare ne na daƙile laifukan intanet a ƙasar, ya sa kai ga kama mutum 130 da ake zargi, 113 ‘yan ƙasashen China da Malaysia ne kuma 17 ‘yan Nijeriya ne. An samu waɗannan mutane da hannu a nau’ukan laifukan intanet iri-iri ciki har da zamba ta intanet da kutse da fasaha mai zurfi da sauran laifukna intanet mai yi wa tsaron Nijeriya zagon ƙasa.”
Sanarwar ta ƙara da cewa an same su da laifi ne bayan an gabatar da hujjoji na intanet da ke alaƙanta su da laifukan intanet.
Hundeyin ya kuma ambato Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, yana bayyana lamarin a matsayin wani muhimmin mataki a ƙoƙarin rundunar na yaƙar laifukan intanet a Nijeriya.
“Ya jaddada cewa samunsu da waɗannan laifuka zai zama izina mai ƙarfi ga ƙungiyoyin masu laikata laifukan intanet na gida da na ƙetare cewa Nijeriya ba za ta kasance mafaka ga laifukan intanet ba.
“Sufeto Janar Egbetokun ya kuma tabbatar wa mutane cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da fasaha ta zamani da ƙarfafa aiki tare da ƙasashen waje da kuma ci gaba da mayar da hankali kan bincike da gurfanarwa domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifukan intanet da kuma tabbatar da an hukunta masu aikata laifukan,” in ji shi.