Malaman addinin Musulunci daga faɗin Arewacin Nijeriya sun kammala wani taro na rana guda a Kaduna, wanda suka kira mai mahimmanci a halin da yankin ke ciki a yanzu.
Malamai daga ƙungiyoyin Musulunci daban-daban da sarakuna da ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron, wanda maƙasudinsa shi ne haɗa kai don ɗaukar matakan magance matsalar tsaro da ke ta’azzara da ta tattalin arziki a yankin
Ga muhimman batutuwan da aka tattauna a wajen taron:
Gano hanyar magance matsalar tsaro
Mahalarta taron sun yi musayar ra’ayoyi a kan yadda za a gano ainihin musabbabin matsalar tsaro da ta addabi arewacin Nijeriya tare da lalubo hanyoyin magance ta da kuma rawar da shugabannin addini ya kamata su taka don gano mafita mai ɗorewa.
Daga cikin malaman da suka yi tsokaci kan hakan har da Dr Bashir Aliyu Umar na Kano, ya yi ta’aliƙi a kan ƙaruwar satar mutane da ‘yan fashin daji da matsin tattalin arziki a faɗin yankin.
Malamin ya jaddada buƙatar malaman addini da shugabannin siyasa da sarakuna su haɗa-kai don ceto rayuka da dawo da zaman lafiya.
“Dole mu ajiye bambance-bambancenmu. Dukkanmu Allah na Ya yi mu. Wannan taron maƙasudinsa shi ne haɗin-kai ba rashinsa ba.
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, wadda jiha ce da ta yi ƙaurin suna kan rashin tsaro, Sanata Abdullaziz Yari ya yabi taron da cewa an yi shi a kan gaɓa, yana mai cewa rashin tsaro ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ne a arewa saboda rashin tsari da rashin damarmakin tattalin arziki da labaran ƙarya.
“Ba zai yiwu mu yi ta zargin gwamnati ba. Mugwaye da ke assasa komai suna cikinmu.
“Dole mu yi aiki tare – daga kan malamai har zuwa ‘yan sauran ƙasa – don kawo ƙrshen wannan bala’i,” in ji Yari.
Sai kuma tsohon gwamnan ya sake yin kira kan a sauya ɗabi’u na tsarin tattalin arziki, yana mai cewa halayyar nan ta neman son yin kuɗi daga sama tana taimakawa wajen ƙaruwar miyagun laifuka da rashin zaman lafiya.
Kokawa kan matsalar shafukan sada zumunta
Sarkin Musulmi, lahaji Sa’ad Abubakar III, shi kuma kira ya yi da a sanya linzami kan amfani da shafukan sada zumunta saboda yadda ake wuce gona da iyaka a amfani da shi.
Ya bayyana damuwa sosai a kan ƙaruwar wuce gona da iri ta hanyar amfani da soshiyal midiya musamman a tsakanin malamai, yana gargadin cewa hakan na jawo babbar barazana ga zaman lafiya da haɗin-kai a Nijeriya.
“Kowa zai iya wayar gari, ya ɗauki wayarsa ya zagi duk wanda yake so, ko wani da ake girmamawa, ko maƙabcinsa ko ma ɗan’uwa. Babu dokoki, babu matakin da za a ɗauka kuma babu mai cewa don me,” a cewar Sarkin Musulmi wanda Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya wakilta.
Shi ma Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana buƙatar a samar da hanyar yin tattaunawa mai ma’ana a soshiyal midiya.
“Daga cikin matsalar har da soshiyal midiya, inda ake samun sa’in’sa sosai, Amma bai kamata mutum ya ƙetare iyakoki ba ta hanyar aibata wasu,” ya ce.
Gumi ya yi gargaɗi a kan sanya a guji haramta amfani da shafukan sada zumunta kwata-kwata amma a tabbatar da amfani da dokokin da ake da su na tafiyar da su.
“Dama kawai dokoki a kan yi wa mutum ɓatanci da sharri. Abin da muke s shi ne waɗannan dokoki a yi amfani da su sosai.”
Haɗin kan Musulmai
Ƙarin abu mai mahimmanci da aka tattauna a kai shi ne inda Sarkin Musulmi ya buƙaci malaman addini da su dage wajen cigaba da yaɗa saƙonnin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmai a fadin ƙasar, bisa ga koyarwar Musulunci.
Shi ma Sheikh Gumi ya jaddada muhimmancin samun tattaunawa a tsakanin bangarorin Musulmi, inda ya yi gargadin cewa tasirin wasu na waje da muradun ma’adinai ne ke rura wutar rashin tsaro a Arewa.
“Wannan taron ba ya adawa da kowa, sai don ci gaban ƙasa. Tattaunawa na da mahimmanci.
“Idan arewacin Nijeriyaya zauna lafiya, to ƙasar gabadaya za ta amfana,” ya ce.
‘Yan majalisar wakilai da na dokoki da suka samu halartar taron sun sha alwashin ba da hadin kai don cim ma muradun taron sosai.