Gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar China ta yaba wa gwamnatin Nijeriya bisa nasarar ceto ‘yan kasarta huɗu da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara.
Ayyukan ceton, wanda Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS), Sojojin Nijeriya da ƴan sanda suka gudanar tare, ya kai ga kuɓutar da waɗannan ‘yan kasar ta China ba tare da matsala ba.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga ne suka yi wa masu haƙar ma’adinai na ƙasar China kwanton-ɓauna a hanyar zuwa wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Saminaka na Jihar Kogi.
A wajen miƙa waɗanda aka ceto a birnin Abuja, Jakadan Chinar a Nijeriya, Yu Dunhai, wanda ƙaramin jakadan ta ƙasar Wang Jun ya wakilta, ya yaba wa hukumomin tsaro na Nijeriya, musamman DSS, saboda saurin ɗaukar mataki bisa bayanan sirri.
Haka kuma ya gode wa hukumar saboda bai wa waɗanda aka ceto kulawar ta kiwon lafiya ta musamman a cibiyar DSS da ke Abuja.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga ne suka yi wa masu haƙar ma’adinai na ƙasar China kwanton-ɓauna a hanyar zuwa wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Saminaka na Jihar Kogi.
A halin yanzu, DSS tana ci gaba da gudanar da ayyukan farautar ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin ƙasar, inda kwanan nan ta samu nasarori da dama — ciki har da kama makamai da harsasai a Jihar Delta — inda ake yaba mata a matsayin shaida ta jajircewar hukumar wajen kare tsaron ƙasa da lafiyar jama’a.